COVID-19: ’Yan majalisar Borno sun ba da albashinsu
’Yan Majalisar Dokoki ta Jihar Borno sun sadaukar rabin albashinsu na wata biyu ga gwamnatin jihar domin ta karfafa yunkurin da take yi hana cutar coronavirus yaduwa. Shugaban majalisar, Abdulkarim Lawan, shi ne ya bayyana hakan ranar Asabar lokacin da ya jagoranci wasu abokan aikinsa suka kai ziyara wa Mataimakin Gwamna kuma Shugaban Kwamitin Cika-Aiki […]
’Yan Majalisar Dokoki ta Jihar Borno sun sadaukar rabin albashinsu na wata biyu ga gwamnatin jihar domin ta karfafa yunkurin da take yi hana cutar coronavirus yaduwa.
Shugaban majalisar, Abdulkarim Lawan, shi ne ya bayyana hakan ranar Asabar lokacin da ya jagoranci wasu abokan aikinsa suka kai ziyara wa Mataimakin Gwamna kuma Shugaban Kwamitin Cika-Aiki Kan Yaki da Cutar Coronavirus, Umar Usman Kadafur, a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
Shugaban majalisar ya yaba wa matakan da gwamnati take dauka domin hana yaduwar wannan cuta, yana mai cewa “kafa wannan kwamitin wani babban hangen nesa ne don ganin an yi wa tufkar hanci”.
Hakazalika ya yaba wa kokarin kwamitin na shiga sako da lungu don fadakar da jama’a a kan hanyoyin kare kai da kuma muhimmancin tsafta.
A jawabinsa, mataimakin gwamnan ya gode wa ’yan majalisar, sannan ya ce hakika hakan wata babbar sadaukarwa ce ga al’ummarsu, kuma su wakilai ne na gari na jama’ar da suka zabe su.
Ya kuma ce ba adadin kudin ne abin dubawa ba, amma hikimar da ke cikin yin hakan.
Sannan ya ba su tabbacin za a yi amfani da kudin yadda ya kamata, kuma kwamitinsa zai ci gaba da hada kai da majalisar wajen yaki da wannan annoba.