COVID-19: Yawan sabbin majinyata a Najeriya ya dan ragu

Bayan da aka jera kusan kwana biyar ana samun sabbin majinyata daga sama da 230 zuwa sama da 300 a Najeriya, an dan samu ragi a yawan wadanda suka kamu, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan suka nuna. Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 12 ga […]

COVID-19: Yawan sabbin majinyata a Najeriya ya dan ragu

Daya daga cikin motocin daukar marasa lafiya da hukumar NCDC ke amfani da su don kai majinyata wurin killace su (Hoto: Twitter/NCDC)

Bayan da aka jera kusan kwana biyar ana samun sabbin majinyata daga sama da 230 zuwa sama da 300 a Najeriya, an dan samu ragi a yawan wadanda suka kamu, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan suka nuna.

Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 12 ga watan Mayu dai ta nuna cewa mutum 146 ne suka kamu, lamarin da ya kai jimillar wadanda aka tabbatar zuwa 4,787.

Hukumar ta NCDC ta kuma ce a cikin wannan adadi an rasa mutum 158; yayin da aka sallami 959 bayan sun warke.

Hakan dai na nufin a yanzu haka akwai mutum 3,828 da ke jinya.

Daga cikin sabbin majinyatan dai 57 a jihar Legas suke, 27 a Kano, 10 a Kwara.

Sai kuma mutum tara a jihar Edo, takwas a Bauchi, bakwai a Yobe, hurhudu a Kebbi da Oyo.

A jhohin Katsina da Neja kuma akwai mutum uku ko wacce, yayin da Filato da Borno da Sakkwato da Binuwai ke da mutum bibbiyu, Gombe da Enugu da Ebonyi da Ogun da Ribas da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya ke da mutum guda ko wacce.

Jihar Legas ce dai ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar da mutum 1,990, sai Kano mai 693, sannan Yankin Babban Birnin Tarayya mai 360.