COVID-19: Yawan wadanda suka kamu a Najeriya ya haura 1,500

Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 1,500, a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC. A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce adadin ya haura ne bayan da aka samu sabbin kamuwa mutum 195. “Zuwa karfe 11.50 na daren 28 […]

COVID-19: Yawan wadanda suka kamu a Najeriya ya haura 1,500

Daya daga cikin dakunan binciken NCDC inda ake gwajin cutar coronavirus

Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 1,500, a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce adadin ya haura ne bayan da aka samu sabbin kamuwa mutum 195.

“Zuwa karfe 11.50 na daren 28 ga watan Afrilu, an samu mutum 1,532 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji NCDC.

Ta kuma kara da cewa daga cikin wannan adadi an sallami mutum 255, yayin da 44 suka riga mu gidan gaskiya.

Tamanin daga cikin sabbin kamuwar dai a jihar Legas suke, 38 a Kano, 15 a Ogun, 15 a Bauci, 11 a Borno.

An kuma samu mutum 10 a Gombe, tara a Sakkwato, biyar-biyar a Edo da Jigawa, biyu a Zamfara, dai-dai a Yankin Babban Birnin Tarayya da Ribas da Enugu da Delta da kuma Nasarawa.

A gaba daya dai jihar Legas ce ta fi yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da mutum 844, sai Yankin Babban Birnin Tarayya mai mutum 158, sannan jihar Kano mai mutum 115.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi