COVID-19: Yawan wadanda suka kamu ya karu da 38
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 38. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter. Ashirin da uku daga cikin mutanen dai a Kano aka same su, biyar a Gombe, […]
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 38.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ashirin da uku daga cikin mutanen dai a Kano aka same su, biyar a Gombe, uku a Kaduna, biyu a Borno, biyu a Abiya, daya a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Sakkwato, daya kuma a Ekiti.
“Zuwa karfe 11.10 na daren 20 ga watan Afrilu an tabbatar da mutum 665 ne suka kamu da cutar COVID-19; daga cikinsu an sallami mutum 188, 22 kuma sun riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.
Jihohin Sakkwato da Gombe da Abiya ne wurare na baya-bayan nan da aka tabbatar da samun wadanda suka kamu.
Jihar Legas, mai mutanen da suka kamu 376, ke kan gaba, sannan Yankin Babban Birnin Tarayya mai mutane 89, sai kuma jihar Kano da mutane 59.