COVID-19: Za a tallafa wa ma’aikatan kamfanoni a Indonesiya

Indonesiya za ta raba wa ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni a kasarta tallafin Dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 500. Gwamnatin kasar ta ce duk wani ma’aikaci a kasar da albashinsa bai haura Dala 343.64 (kimanin N150,000) ba a wata, zai samu karin albashi a matsayin tallafin COVID-19. Ministan Masana’antu, Erick Thohir ya ce tallafin […]

COVID-19: Za a tallafa wa ma’aikatan kamfanoni a Indonesiya

Shugaban Kasar Indonesiya, Joko Widodo

Indonesiya za ta raba wa ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni a kasarta tallafin Dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 500.

Gwamnatin kasar ta ce duk wani ma’aikaci a kasar da albashinsa bai haura Dala 343.64 (kimanin N150,000) ba a wata, zai samu karin albashi a matsayin tallafin COVID-19.

Ministan Masana’antu, Erick Thohir ya ce tallafin wani yunkuri ne na bunkasa tattalin arzikin magidanta da kyautata rayuwarsu a lokacin COVID-19.

Ya bayyana cewa za a ba da tallafin Dala 41 (fiye da N20,000) a duk wata na tsawon wattani hudu ga wadanda za su amfana a dukkan ma’aikatun gwamnati da kamfanoni.

Ministan Kudin Sri Mulyani ya ce kasar ta ware kudaden ne a yunkurinta na rage wa ‘yan kasarta illar da COVID-19 ta yi wa rayuwarsu.

Indonesiya ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki arziki a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram