COVID-19: Za a wallafa sunayen majinyatan da suka gudu a Kano

Kwamitin kar ta kwana da ke yaki da annobar coronavirus a jihar Kano ya yi barazanar wallafa sunayen majinyatan nan guda biyun da suka kamu da cutar suka kuma cika wandonsu da iska bayan da aka aike da su wurin killace wadanda suka kamu. Jami’in tsare-tsare na kwamitin, Dokta Tijjani Usaini, shi ya bayyana haka […]

COVID-19: Za a wallafa sunayen majinyatan da suka gudu a Kano

Kwamitin kar ta kwana da ke yaki da annobar coronavirus a jihar Kano ya yi barazanar wallafa sunayen majinyatan nan guda biyun da suka kamu da cutar suka kuma cika wandonsu da iska bayan da aka aike da su wurin killace wadanda suka kamu.

Jami’in tsare-tsare na kwamitin, Dokta Tijjani Usaini, shi ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da manema labarai.

Tun a ranar Litinin ne aka tabbatar mutanen uku suna dauke da cutar bayan da aka yi musu gwaji, sai dai tun daga wannan lokaci ba a sake jin duriyarsu ba.

Rahotanni sun bayyana cewa daga baya an gano mutum daya daga cilkinsu kuma tuni aka killacce shi a wata cibiya da ke birnin na Kano.

Yanzu haka dai kwamitin yana neman sauran mutanen biyu ruwa a jallo.

Dokta Tijjani ya bayyana cewa matakin wallafa sunaye tare da hotunan marasa lafiyar zai bayar da damar kama su tare kuma da killace su don hana bazuwar cutar a tsakanin alummar jihar.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu