COVID-19: Za a yi wa tsofaffi gwajin dole

Za a bi ‘yan sama da shekara 65 gida a yi musu gwajin COVID-19 na tilas.

COVID-19: Za a yi wa tsofaffi gwajin dole

Daya daga cikin dakunan binciken NCDC inda ake gwajin cutar coronavirus

Za a yi wa tsofaffi ‘yan shekara 65 zuwa sama gwajin cutar coronavirus na dole a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Shugaban kunigyar gwamnonin yankin, Dave Umahi na Jihar Ebonyi ya ce sun amince su dakatar da bude makarantu a yankin, amma za su dukufa wajen sauya tsarin makarantun su dace da tanade-tanaden hukumar NCDC da ke yaki da cututtuka masu yaduwa.

“Za mu bi gida-gida domin gano tsofaffi ‘yan sama da shekara 65 domin a yi musu gwajin COVID-19 na wajibi a fadin yankin Kudu maso Gabas.

“Muna kira ga malaman addini da shugabannin kananan hukumomi da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka domin samun nasara”, inji shi, da yake bayani game da taron da suka yi ta bidiyo.

“Mun yi zuzzurfan tattaunawa game da bude makarantu kuma muna da fargaba musamman a kan makarantun nazare da firamare, don haka muka amince a yi wa dukkan malamai gwajin cutar a kuma sauya tsarin karatu domin su dace da dokokin NCDC.

“Za mu yi hakan, amma za mu jira Gwamnatin Tarayya ta sanar da lokacin da za bude makarantu”, inji Umahi.

Ya kara da cewa gwamnonin yankin sun amince su tura jami’an lafiya zuwa makarantu domin su yi aikin wayar da kai game da hanyoyin kariya daga cutar ta COVID-19.