‘COVID-19 za ta kara wa talakawa talauci’

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda annobar COVID-19 ke jefa talakawa cikin karin talauci a duniya. Yayin jawabinsa ta bidiyo a taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan hanyoyin magance talauci a duniya, shugaban ya koka da cewa kashi goma cikin 100 na mutanen duniya na cikin tsananin talauci. COVID-19 ta kashe mutum […]

‘COVID-19 za ta kara wa talakawa talauci’

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda annobar COVID-19 ke jefa talakawa cikin karin talauci a duniya.

Yayin jawabinsa ta bidiyo a taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan hanyoyin magance talauci a duniya, shugaban ya koka da cewa kashi goma cikin 100 na mutanen duniya na cikin tsananin talauci.

A cewarsa, COVID-19 ta sa mutanen Najeriya da ke fama da talauci iri-iri kara talaucewa, duk da cewa gwamnati na kokari wajen shawo kan talaucin da kuma taimaka wa sana’o’in talakawa.

Shugaban MDD Farfesa Tijjani Muhammad-Bande ya shirya taron ne domin ya zamo harsashin hadin gwiwa domin rage talauci a duniya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno