COVID-19: Yawan wadanda suka kamu a Najeriya ya haura 1,000
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 1,000. Adadin dai ya kai haka ne bayan da aka samu sababbin kamuwa da cutar har mutum 114. Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ne suka nuna hakan. […]
Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya haura 1,000.
Adadin dai ya kai haka ne bayan da aka samu sababbin kamuwa da cutar har mutum 114.
Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter ne suka nuna hakan.
“Zuwa karfe 11.30 na daren 24 ga watan Afrilu akwai mutum 1,094 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji NCDC.
- Dokar hana fita: Abu uku da suka yi wa matan Kano dadi
- COVID-19: Gidajen rediyo da talabijin 40 za su durkushe
Haka kuma yawan wadanda suka rasu ya karu da mutum daya.
Tamanin daga cikin mutanen da suka kamu a baya-bayan nan a jihar Legas suke, 21 a Gombe, biyar a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a Zamfara, biyu a Edo, daya a Ogun, daya a Oyo, daya a Kaduna, daya kuma a Sakkwato.
A cewar NCDC, daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu mutum 208 aka sallama, yayin da 32 suka riga mu gidan gaskiya.
Zuwa tsakar daren na 24 ga wata dai an tabbatar da samun mutanen da suka kamu da COVID-19 a jihohin Najeriya 27 da Yankin Babban Birnin Tarayya.
Wadda ta shiga lissafi a baya-bayan nan ita ce Zamfara.