Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United
Kungiyoyi sun fara tuntubar Cristiano Ronaldo, dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye Manchester United a kakar wasannin 2021/2022
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Cristiano Ronaldo, na shirin barin ta a kasuwar cinikin ’yan wasa ta bana.
Kafar yada labaran wasanni ta ESPN ta ce shahararren dan wasan na neman kungiyar da zai koma ne a daidai lokacin da sabon kocin kungiyar, Erik ten Hag, yake shirin yin sabbin sauye-sauye.
- Liverpool da Bayern Munich sun cimma matsaya kan cinikayyar Mane
- Yajin aikin ASUU ba shi da wata fa’ida —JAMB
ESPN ta ruwaito kafar La Republic ta kasar Italiya na cewa dan wasan mai shekara 39 zai bar Manchester United ne saboda tunanin sauye-sauyen za su yi mishi tarnaki, ganin cewa za su fi yin tsauri ne a kan ’yan wasan gaba.
A yayin da ake jiran bude kasuwar cinikin ’yan wasa, manajan dan wasan, Jorge Mendes, na neman kungiyar da ta fi dacewa ya koma a nahiyar Turai kuma tuni kungiyar Roma da Sporting CP suka fara tattaunawa da shi.
Roma ta fara zawarcin dan wasan ne tare da tunanin tasirin kocinta, Jose Mourinho, zai taimaka wajen shawo kan dan wasan.
A daya bangaren kuma, Sporting CP na kyautata zaton Cristiano Ronaldo, wanda tsohon dan wasanta ne zai dawo wajenta.
A baya Ronaldo ya yi wasa a Sporting CP kafin ya koma Manchester United a 2003.
A kakar wasa ta 2021/22 da aka kammala dan wasan shi ne ya fi zura kwallaye a Manchester United inda ya ci kwallo 24 a wasanni 37 da ya buga wa kungiyar.