Cristiano Ronaldo ya bude gidan ajiye kayan tarihinsa
Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya bude gidan ajiye kayayyakin tarihinsa a garin Madeira da ke Fotugal.Gidan tarihin, katafaren gini ne mai dauke da dakuna 125.dan kimanin shekara 28, Ronaldo da yanzu haka yake cikin sahun ’yan kwallo uku da za su fafafata a gasar […]

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya bude gidan ajiye kayayyakin tarihinsa a garin Madeira da ke Fotugal.
Gidan tarihin, katafaren gini ne mai dauke da dakuna 125.
dan kimanin shekara 28, Ronaldo da yanzu haka yake cikin sahun ’yan kwallo uku da za su fafafata a gasar gwarzon dan kwallon duniya ya ce ya yanke shawarar gina gidan ajiyar kayayyakin tarihinsa ne saboda masu son yin nazarin tarihin rayuwarsa daga ko’ina a fadin duniya.
Shi dai Ronaldo ya taba lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Duniya a shekarar 2008 a lokacin da yake buga kwallo a kulob din Manchester United da ke Ingila.
Kafin ya bar kulob din ya lashe kofin gasar rukunin Premier har sau uku sannan ya lashe kofin kalubale sau daya, ya lashe kofin Kalin (Carling) sau biyu sannan kuma ya lashe kofin Club World Cup sau daya.
Bayan ya canza sheka zuwa kulob din Madrid da ke Sifen a 2009 ya samu nasarar lashe gasar rukunin La-Liga sau daya da kofin Sarki (Copa del Rey) sau daya.
Daga cikin kayayyakin tarihin Ronaldo akwai kyautar da ya lashe ta wanda ya fi zura kwallaye a raga a kulob din Andorinha da ke Fotugal a lokacin yana da shekara takwas.