Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan nasarar zura kwallo
‘Yan kallo suka barke da sowa da murna bisa abin da ya yi.
Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan ya zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta Al Shabab a Gasar cin Kofin Kwararru wato Saudi Pro League da ake yi a Saudiyya.
Galibi dai an fi samun musulman ’yan kwallon kafa da yin sujjada domin nuna godiya da girmamawa ga Allah da kuma bayyana farin cikin zura kwallo.
- Gwamnan Kwara ya zama sabon Shugaban Kungiyar Gwamnoni
- WhatsApp ya bullo da tsarin gyara saƙon da aka aika — Zuckerberg
A fafatawar ta mako na 28 a ranar Talata, Ronaldo ya ci wa Al Nassr kwallo ta uku a minti na 59 sannan ya yi sujjada a filin wasa na KSU da ke Riyadh, kuma nan take ‘yan kallo suka barke da sowa da murna bisa abin da ya yi.
Hotunan bidiyo da suka karade dandalan sada zumunta sun nado yadda dandazon ‘yan kallo suka rika sowa da murna a yayin da shahararren dan kwallon kafar ya rusuna ya yi sujjada bayan ya ci kwallo.
‘Yan wasan Al Nassr Anderson Talisca da Abdurrahman Garib kowane ya zura kwallo daya, yayin da Cristian Guanca ya ci wa Al Shabab abin da ya sa aka tashi da ci 3-2.
Lamarin ya janyo cece-kuce
Lura da yadda tauraron ya yi salon murnar da ba a taba ganin wani wanda ba musulmi ba ya yi irinta walau bayan nasarar zura kwallo ko don wata murna daban.
Salon murnar kwallon na Ronaldo dai ya kayatar da dimbin magoya bayansa musamman a cikin kasar ta Saudi Arabia da ya koma takawa leda a farkon shekarar nan bayan rabuwa da Manchester United.
Wasu faifan bidiyo dai sun nuna yadda dan wasan mai shekaru 38 bayan zura kwallon kamar yadda ya saba, ya yi fitaccen salon murnar da aka fi sanin shi da ita, wato SIUU sannan ya kara da sujjada, lamarin da ya sanya ilahirin filin wasan karade da sowa.
Wannan murna ta Ronaldo dai ta zamo babban batun tattaunawa tare da tafka muhawara a dandalin sada zumunta.
Yanzu Al Nassr tana da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta Saudiyya.