Croatia ta doke Maroko a neman mataki na 3 a Gasar Cin Kofin Duniya
Maroko ta yi rashin nasara ne da ci biyu da daya
Tawagar kasar Croatia a ranar Asabar ta doke takwararta ta kasar Maroko da ci biyu da daya a fafatawar neman mataki na uku a Gasar Cin Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Dan wasan Croatia, Josko Gvardiol, shi ne dai ya fara zura wa kasarsa kwallo a raga bayan minti bakwai da take wasan, wanda aka fafata a filin wasa na Khalifa, amma Achraf Dari ya farke tun ba a je ko ina ba.
- Sabbin takardun kudin da CBN ya fitar sun kare tatas a bankuna
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 6 a Borno
Sai dai kwallon da Croatia ta kara jefawa a karo na biyu tun kafin zuwa hutun rabin lokaci ya sanya ta zama kasa ta uku a gasar, wacce karo na 11 ke nan wata kasa daga nahiyar Turai na kammalawa a matakin.
A nata bangaren kuwa, Maroko ita ce kasar Afirka ta farko a tarihi da ta taba zuwa matakin wasan dab da na karshe tun da aka fara gasar.
Yanzu dai ranar Lahadi mai za a fafata wasan karshe a gasar tsakanin kasashen Faransa da Argentina.
Wannan dai shi ne karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa da ke yankin Gabas ta Tsakiya da ta shirya gasar tun da aka fara ta a tarihi a sherar 1930.