Cross River: Jihar da babu coronavirus

Har zuwa tsakar daren Litinin, akwai jihohi biyu a Najeriya wadanda bayanan hukuma ke nuna ba su da wandada suka kamu da coronavirus ko daya—Kogi da Kuros Riba. Jihar Kuros Riba dai ta fara daukar matakin hana cutar yaduwa ne lokacin da ta killace al’umma sannan ta kafa dokar sanya amawali wato takunkumin rufe fuska, […]

Cross River: Jihar da babu coronavirus

Dokta Betta Edu, Kwamishinar Lafiya ta jihar Kuros Riba

Har zuwa tsakar daren Litinin, akwai jihohi biyu a Najeriya wadanda bayanan hukuma ke nuna ba su da wandada suka kamu da coronavirus ko daya—Kogi da Kuros Riba.

Jihar Kuros Riba dai ta fara daukar matakin hana cutar yaduwa ne lokacin da ta killace al’umma sannan ta kafa dokar sanya amawali wato takunkumin rufe fuska, kamar yadda Dokta Betta Edu, kwamishinar lafiya ta jihar, ta shaida wa Aminiya.

“Babban matakin da muka fara dauka shi ne na killace al’ummar jihar nan gaba daya na tsawon mako biyu, sannan muka tilasta yin amfani da amawalin rufe fuska a wuraren kasuwanci ko inda jama’a ke taruwa, muka raba musu kayayyakin wanke hannu da man tsaftace hannu (sanitizer), kuma muka matsa wajen yin gangami birni da kauye”, inji ta.

Karin matakai

Nan da nan gwamnatin jihar ta sanya aka saka amawalin aka rika raba shi ga al’umma, yayin da wasu mutane kuma suka rika dinkawa suna sayar wa jama’a.

Amma kuma ba Kuros Riba ba ce kadai jihar da ta killace mutane—wasu jihohin ma sun yi haka, amma suna da masu dauke da cutar.

“Mun sanya ’yan sintiri su kula mana da iyakokin mu, musamman tsakaninmu da Kamaru da muka ji su ma ta bulla musu a can.

“Muna bin dare muna duba manyan hanyoyin da ke makwabtaka da mu.

“Bayan haka mun kara killace kanmu na wasu mako biyun, amma ba mu hana jama’a su yi walwala ba.

“To daukar wadancan matakai na tun wuri hakika mun ga sakamako mai kyau duk da a wurin wasu mutanen an takura su”.

Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River
Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba sanye da amawalin da aka yi da kyallen rigar jikinsa

Jihar ta kuma killace hanyoyin shiga da fita na makwabtan jihohi a ko wacce karamar hukuma sannan kuma a manyan hanyoyi da tituna aka baza jami’an tsaro masu kula da wadanda ba su sanya amawalin ba—duk wanda aka kama bai sanya ba zai biya tara ta N300,000.

Tarukan jama’a

Ba ta tsaya a nan ba, gwamnatin ta hana taruka  da duk wata sabga ta jama’a bayan da ma ta dakatar da Musulmi da Kirista zuwa wuraren ibadun su.

Wani mataki da ka iya nuna muhimmancin da gwamnatin jihar ta bai wa killace jama’a shi ne a watan jiya, lokacin da wasu jami’an Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) suka yi niyyar kai ziyara jihar, Ms Edu ta ce sai an killace su har tsawon kwana 14.

A lokacin dai an ambato ta tana cewa jihar ta fi sha’awar ta hana cutar bayyana a kan ta kula da wadanda suka kamu.

“Mun riga mun rufe iyakokinmu da duk hanyoyin shigowa don kauce wa yaduwar kwayar cutar. Ba lallai ba ne sai ta shiga dukkan jihohi.

“Gwamnatin jiha tana dukkan mai yiwuwa don tabbatar da cewa ba mu da COVID-19. Manufarmu ta tilasta saka amawali ko takunkumin rufe fuska ta taimaka matuka wajen cimma wannan nasara”, inji ta.

An takura

Game da mutanen da aka takura saboda killace jama’a da aka yi kuwa, gwamnatin jihar ta raba tallafin kayan abinci a gundumomin siyasa uku na jihar.

Alhaji Sha’aban Abdullahi, wani mazaunin jihar ta Kuros Riba, ya shaida wa Aminiya cewa, “An takura jama’a, an ji jiki kafin gwamnati ta ba mutane tallafin kayan abinci.

“Kowa ya kosa amma daga baya ga shi an ji dadin jajircewar da hukumar ta yi mana tun da ga shi Allah Ya kare mu matakan sun yi daidai”.