Cuta daban, magani daban

Shan magani barkatai ya zama ruwan dare,  amma ba lallai a samu lafiya ba! Yayin da aka je wajen wani likitan sai ka je ya ce a sha wani magani daban sabanin wanda na farko ya rubuta! Hakan ya sa mutane da dama na fama da wasu cuttutuka a dalilin shan magani daban da cuta. […]

Cuta daban, magani daban
Cuta daban, magani daban

Shan magani barkatai ya zama ruwan dare,  amma ba lallai a samu lafiya ba! Yayin da aka je wajen wani likitan sai ka je ya ce a sha wani magani daban sabanin wanda na farko ya rubuta! Hakan ya sa mutane da dama na fama da wasu cuttutuka a dalilin shan magani daban da cuta. Hakan ya sa sai an rasa yadda za a yi sai masu dama su bar kasar don kulla da lafiyar su, yayin da a kasashen waje sai ka ji an ce wai a dalilin shan magani mutum ya kamu da cutar da aka fitar da shi wajen, a ji sunan wata cuta! inda za a wa marasa lafiyar sabon gwaji da sabon magani.
Da farko matsalar nan ta likitoci ce ko jami’an da suke kulla da kiwon lafiya, musamman sau da yawa sai ka iske daliban kiwon lafiya ko ‘yan makarantun nas da ungozuma na sharholiyarsu ba su mayar da hankali wajen samun ilimin ba, wasu ma da ka gansu za ka ga ne ba su da natsuwa, inda ake mayar da irin wadannan makarantun mattatarar karuwanci, da dare ya yi sai a je a debo wasu kuma su fita farautarsu.
Hakan ya sa wasu ma basu yadda da nas-nas ba, balle su yadda a masu allura. Irin wadannan matasan masu sayar da magani ko harkar kiwon lafiya kan ba matasa ‘yan makaranta kayan maye ko magununwan da zasu zubar da ciki.
Wasu ma likitoci da jami’an kiwon lafiya na da takardun bogi, a haka zasu rika kashe mutane sai ranar da dubu ta cika!, wannan dabi’a ta sa cuttutukan da ba a san su ba a da suka yawaita, a yau ciwon siga, ciwon hanta, ciwon kwada ko ciwon hunhu sun zama ruwan dare, sai ka iske matashi da hawan jini!
Ana samun matsaloli wajen magungunan da ake shigowa da su kasar nan, domin sai ka sayi magani daga wata kasa amma da ka sha daya sai cutar ta gudu, amma maganin Najeriya sai ka shanye baki daya ka ji da sauran cutar! Ko wani ya je waje ya shigo da wadanda ba su da karfi ko karko don ya ci riba a kasar! Dole sai hukumar kulla da abinci da magani (NAFDAC) ta sai do game da irin magugunan da  ake shigo da su kasar da kimist din da ake hada su, ta yadda za a yi aiki tare da hukumar yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA) don a shawo kan wannan matsalar da ke kashe al’umma.
Harkar magani na da muhimmanci, musamman ganin an fi samun kudi akan ta fiye da kowane irin kasuwanci! Muhimmancinta ya sa a wasu kasashe gwamnati ke tafiyar da harkar magani da kiwon lafiya, ko a ba mutane dama, sa masu ido ake yi. Amma mu a nan wasu kan mayar da kansu ‘yan harkar 100 bisa 100, duk da hadarin ta ita ce mutane za a rika cuta, kuma akwai hakki, sannan akwai illa a dogon zango. Duk da cewa wasu cuttutukan na kama kamar amosanin kai da mura ko numoniya, a haka sai an karfafa bincike kafin a tabbatar wace cuta ta kama marasa lafiya, musamman a irin halin da muka tsince kanmu da lalacewa muhalli, cin gurbaceccen abinci da yanayi mai azabtarwa.
Tabbas karatu a waje ya taimaka kuma ya kawo cikas, domin dalibai da dama ba su san sunayen maganuna ba!, musamman wadanda suka yi karatu a wasu kasashe sabanin wadanda ake yin Turanci, sai ka iske mutum ya karanta likita amma sai nas su rika gaya masa abin da ya kamata yi, ko maganin da ya kamata ya bayar! Wata matsala ita ce ta karancin ma’aikatan kiwon lafiya da likitoci, idan aka kwatanta da yawan mutanen da suke dubawa a rana guda, sai ka iske likita daya daga safe har dare, in ma akwai likita asibitin ke nan!
Amma wannan duk ba wata matsala ba ce idan ana da niyyar ci gaba. Misali kukan karancin ‘yan sanda kuma ana fama da rashin tsaro ai a ganina sai a dauki dubannin matasa aiki, ta yadda za a samu wadanda za su rika aikin dare ma, to haka abin yake a asibitoci; me zai hana a dauki nauyin yara su karanta wannan bangare a cikin gida da waje, kuma a kwadaitar da daliban da kyaututuka da albashin da ake samu idan an yi wannan aiki.
Dole sai an kara neman ilimi kuma a kiyaye, don aikin kiwon lafiya amana ce. Akan haka sai an kawo kayan aiki na zamani da dakunan gwaje-gwaje, ta yadda za a gane ainihin me yake damun mara lafiya, a
gurguje za a rubuta wa mutum magani ko a gaggauta ba shi magani, ko a dirka masa allura a sunana gama da shi wani ya shigo asibitin!
Sannan wani lokaci garin burgewa sai a kara wa mutum yawan abin da zai sha don rage radaddin cuta bayan haka ya saba ka’idar maganin ko sai a rubuta wa mutum magani daban sai mai sayar da maganin ya ce ba wannan amma akwai wannan kuma aikinsu daya, bayan ba haka aka gaya masa a asibiti ba. Bayan da dama daga cikin masu sayar da maganin nan za ku iske su ba ilimi, ba lasisi sai su fito gwada sa’a. Inda wani lokaci su kan koya wa  yara batsa, sannan su ba matasa maganin karfin maza da kara kuzari su jarraba, wanda haka kan kai wasu da dogara da wadannan sinadari masu illa Sannan a gargadi maras sa lafiya don sau da yawa su kan fada tarkon masu sayar da magani! Wani lokaci da mutum ya dan sami dauki sai ya watsar da sauran magungunan, yayin da wani lokaci akan sha kwayoyi don wartsakewa!
Ganin kyamis duk inda ka je, shi ma ya taimaka wajen yada miyagun kwayoyi, musamman don gwamnati ba ta bin didigin lamarin, don a kasa yaki da zazzabin cizon sauro, wanda yana daya daga cikin cuttutukan da suke kasha mutane a nahiyar Afrika.
Ya kamata a bar yin siyasa wajen ba mutum ministan ilimi ko kwamishina, a tabbatar da an lura da aikin da ya yi a bangaren, kuma yaya bar asibitin da ya yi aiki, kuma shin shagonsa na da arha da kawo magungunan masu inganci? Ko ya ake tafiyar da marasa lafiya a asibitin da ya bude ba wai jam’iyya ba ko dan gani kashenin masu zartarwa domin da ilimi da kiwon lafiya sun wuce wasa da su ake gina al’umma.
Buhari Daure
Muryar Talaka
+2347035986444
[email protected]

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna