Cutar ƙyanda ta laƙume rayuka 42 a Adamawa

Cutar ƙyanda ta ɓarke a unguwanni 8 a Mubi da kuma unguwanni 7 a Gombi.

Cutar ƙyanda ta laƙume rayuka 42 a Adamawa

Aƙalla mutane 42 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ƙyanda a ƙananan hukumomin Mubi da Gombi a Jihar Adamawa.

Kwamishinan lafiya da ayyukan jin ƙai, Feliɗ Tangwame ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Juma’a.

Tangwame ya bayyana cewa, cutar ƙyanda ta ɓarke a unguwanni 8 a Mubi da kuma unguwanni 7 a Gombi, inda ya ƙara da cewa “ adadin waɗanda suka mutu ya kai 42 daga cikin 131 da kuma 177 da suka kamu da cutar a Mubi da Gombi.”

Duk ƙananan hukumomin jihar in banda Lamurde an sanya su a matsayin waɗanda cutar za ta iya ɓulla.

Sai dai Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta ɗauki matakin shawo kan cutar, inda ta shawo kan lamarin cikin gaggawa.

Ya ce, gwamnati da abokan hulɗarta na sanya ido sosai a kan lamarin, don haka ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da ɗaukar matakan da suka dace kan cutar.