‘Cutar ƙyandar biri na buƙatar matakan gaggawa a Afirka’

Cutar ƙyandar biri ta kama mutum dubu 15, inda mutane 461 suka mutu.

‘Cutar ƙyandar biri na buƙatar matakan gaggawa a Afirka’

Kyandar Biri

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bayyana cutar ƙyandar biri da ta bulla a baya-bayan nan a nahiyar da cewa ta zama matsalar lafiya da ke buƙatar matakan gaggawa.

Sake bullar cutar ƙyandar biri a baya-bayan nan a nahiyar Afirka, na ƙara ba da tsoro a fannin kula da lafiyar al’umma a cikin nahiyar.

Wannan ne ya sanya hukumomi bayyana ta a matsayin wata gagarumar barazana ta lafiya.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta kafa kwamitin ƙwararru na gaggawa da zai tattauna batun wannan cuta da aka gani cikin ƙasashe 18 a Afirka.

Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana damuwa kan yaɗuwar sabuwar nau’in cutar ƙyandar biri, yana mai tabbatar da cewa zai karbi shawara a yau Laraba don ganin ko za a ayyana cutar a matsayin mai matuƙar hadari a faɗin duniya.

Cikin jawabin da ya gabatar a farkon taron gaggawa da hukumar ta yi, ya ce cutar ƙyandar biri na saurin yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da ma makwabtanta.

Ya ce, “A shekarar da ta gabata an samu ƙaruwar waɗanda cutar ta kama, sannan kuma yawan waɗanda suka kamu a shekarar da muke ciki ma ya zarta na bara da dubu 14, sannan an samu mace-mace 524.

“Ɓullar nau’in cutar na Clade 1b da ma yaɗuwarta wanda aka lura da cewa ta hanyar jima’i aka fi kamuwa da ita, an same ta ƙasashe maƙwabtan Congo, abin da ya sa ke nan na ke son ayyana cutar a matsayin mai matuƙar haɗari.

Dokta Tedros, ya ce a watan da ya wuce kadai an samu waɗanda suka kamu da sabuwar nau’in cutar ta Clade 1b a ƙasashe kamar Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda, inda a bara ba a samu bullar cutar ba.

Sai dai ya ce, yanzu suna ƙoƙarin magance ba nau’in Clade ba kawai, har ma kowacce irin nau’i ce.

Dokta Tedros, ya ce WHO ta saki kuɗi har dala miliyan 1 da dubu dari huɗu daga asusunta na ko ta kwana, sannan za ta sake sakin wasu, to amma tana shirin neman taimako domin lura da yaɗuwa da kuma shiryawa cutar.

Ya zuwa yanzu dai cikin wannan shekarar, an samu mutum dubu 15 da suka kamu yayin da mutane 461 suka mutu ita.

Cutar ƙyandar biri ta fara ne daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da samfurin farko na Clade I yayin kuma da aka samu samfuri na biyu na Clade Ib daga bisani da ke da saurin yaduwa musamman a tsakanin kananan yara.

An dai bayyana cewa kwayar cutar ba ta nuna matukar alamu na karfi ba, sai dai kuma tana iya kisa.

Sama da mutum miliyan 10 ne ke bukatar samun allurar rigakafin ƙyandar birin a Afirka a halin yanzu a cewar WHO.