Cutar amai da gudawa na yaduwa a Arewa

Yanzu haka cutar amai da gudawa da ake kira kwalara a takaice tana ci gaba da yaduwa a jihohi daban-daban na Arewa inda ake fuskantar asarar rayuka. An fara samun rahoton bullar cutar ce a sansanin ’yan gudun hijirar rikicin Jihar Nasarawa da ke garin Namu ta karamar Hukumar kua’an Pan a Jihar Filato, inda […]

Cutar amai da gudawa na yaduwa a Arewa
Cutar amai da gudawa na yaduwa a Arewa

Yanzu haka cutar amai da gudawa da ake kira kwalara a takaice tana ci gaba da yaduwa a jihohi daban-daban na Arewa inda ake fuskantar asarar rayuka. An fara samun rahoton bullar cutar ce a sansanin ’yan gudun hijirar rikicin Jihar Nasarawa da ke garin Namu ta karamar Hukumar kua’an Pan a Jihar Filato, inda a ranar Talatar da ta gabata Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato Mista Abraham Yiljap ya tabbatar da mutuwar mutum 11, maimakon 30 da aka rika adawa. Jihar Katsina ta kasance ta baya-bayan nan da aka samu barkewar cutar, inda rahotanni suka nuna cewa akalla mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu ke jinya karbar a asibiti sakamakon barkewar cutar a karamar Hukumar Jibiya. Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya shawarci jama’a su rika kula da abinci tare da wanke hannu kafin cin abincin a matsayin rigakafin cutar. Kwamishinan Dokta Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a tattaunawa manema labarai sakamakon bullar cutar a wasu daga cikin jihohin kasar nan. Ya ce akwai bukatar jama’a su rika wanke kayan marmari da na lambu sosai kafin su ci. Ya ce gwamnati ta tanadi kayan aiki da magunguna da na rigakafin da ake gudanarwa a fadin jihar. Cutar ta haddasa asarar rayuka a jihohin Sakkwato da Zamfara da suke makwabtaka da Jihar Katsina.