Cutar amai-da-gudawa ta barke a Sudan ta Kudu
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa mutane 12 suka mutu bayan barkewar cutar amai-da-gudawa a Sudan ta Kudu wanda kuma take fama da yakin basasa kimanin watanni biyar ke nan.Mai magana da yawun hukumar, Tsrik Jasarebic ya ce cutar ta barke ne ranar Litinin da ta gabata kuma zuwa yanzu an samu labarin […]

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa mutane 12 suka mutu bayan barkewar cutar amai-da-gudawa a Sudan ta Kudu wanda kuma take fama da yakin basasa kimanin watanni biyar ke nan.
Mai magana da yawun hukumar, Tsrik Jasarebic ya ce cutar ta barke ne ranar Litinin da ta gabata kuma zuwa yanzu an samu labarin bullarta yankuna da dama da ke kasar. Ya kara da cewa sun fara aikawa da magunguna yankunan da anobar ta shafa ciki har da babban birnin kasar, Juba.
Asusun Tallafawa Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana aikawa da tanti da kuma magunguna. Hakazalika, kasar Amurka ta bayyana ware Dala miliyan 50 daga asusun kasar na ’yan gudun hijira don sayan kayayyakin agaji wanda za a aika da su kasar.
Rahotanni sun ce akalla ’yan gudun hijira dubu dari uku ne suka ketara kasashen kamar su: Ethiopia da Kenya da Sudan da kuma Uganda. Jumillar ’yan Sudan ta Kudu fiye da miliyan daya ne suka kaurace wa gidajensu dalili da yakin basasa da aka kwashe wata biyar ana fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da mayakan ’yan tawaye da ke karbar umarni daga mataimakin shugaban kasar. Haka kuma fararen hula dubu 79 ne ke samun mafaka a sansanin dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya da kuma wasu fiye da dubu 32 da ke cinkushe a wani sansani na Majalisar dinkin Dinkin Duniya da ke Juba.
Har-ila yau, yanayin damina da ake ciki a kasar na haifar da cikas ga ayyukan agaji a lokaci daya kuma yana kara yaduwar cutar.
Yara ne dai suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar. Amma Hukumar UNICEF ta ce ta yi wa yara akalla dubu 80 da ke kasar allurar rigakafin cutar.
Cutar mai hadari ta na addabar hanji ne tare haifar da hararwa da kuma gudawa. Kuma ta iya kashe akalla mutum takwas cikin goma da suka kamu da ita. Ana iya shawo kanta ne ta hanyar baiwa wanda ya harbu ruwan gishiri da siga.