Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Anthrax tana kama mutane musamman idan sun yi mu’amala da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka sha abin da dabbobin ke samarwa.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da ɓullar cutar Anthrax a Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Nijeriya, Ben Goong ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Mista Goong ya fitar, ya ce an gano cutar a wata gona da ke jihar a Arewa maso Yammacin ƙasar saboda akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wajen lura domin rage yaɗuwa da illar cutar.

“Anthrax, cuta ce da ƙwayar cutar bacterium Bacillus anthracis ke jawowa, kuma tana kama dabbobi irin su shanu da awakai da sauran su.

“Sannan tana kama mutane musamman idan sun yi mu’amala da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka sha abin da dabbobin ke samarwa.

“Daga cikin alamomin cutar akwai zazzaɓi da tari da amai da bushewar maƙogwaro da ciwon kai da ƙaiƙayi da sauran su.

“Duk da cewa akwai rigakafi da ake yi wa dabbobi domin kare yaɗuwar cutar, gano cikin sauri da ɗaukar matakan da suka dace ya fi kyau da saurin daƙile ta.

“Don haka ne muke kira da mutane musamman a jihohin da suke da maƙwabtaka da jihar Zamfara da su ɗauki matakan kariya da ɗaukar hanyoyin domin daƙile yaɗuwarta.”

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa