Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax a karon farko a Najeriya

Dama dai an gargadi ’yan Najeriya tun bayan bullar cutar a Arewacin Ghana.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax a karon farko a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax karon farko a hukumance a Najeriya.

Wata sanarwa ta Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta ce ta samu rahoton dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar Anthrax a wata gona da ke Suleja a Jihar Neja a ranar 14 ga watan Yuli.

Ma’aikatar ta ce lamarin ya faru ne a wata gonar dabbobi da ta kunshi shanu da tumaki da awaki da ke Gajiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Karamar Hukumar Suleja a Jihar Neja.

A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Babban Likitan Dabbobi na Najeriya, Dokta Columba Vakuru, ta ce an samu wasu daga cikin dabbobin dauke da alamomi da suka hada da zubar jini daga sassan jikinsu, hanci, idanu da kunnuwa.

Ta ce tawagar masu bayar da agajin gaggawa da ta hada da kwararrun ma’aikatan lafiya na tarayya da na jihar sun ziyarci gonar don gudanar da bincike na farko tare da tattara samfurori daga dabbobin da suka kamu da cutar.

Ma’aikatar ta ce gwaje-gwaje na Cibiyar Nazarin Dabbobi ta Kasa ta tabbatar da kamuwa da cutar, “wanda ke nuna alamar cutar Anthrax ta farko a Najeriya a cikin ’yan shekarun nan.”

Ta yi nuni da cewa, Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi ga ‘yan Najeriya makonnin da suka gabata bayan samun labarin barkewar cutar Anthrax a Arewacin Ghana, inda duk dabbobin da suka kamu da cutar suka mutu.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta yi kira ga ’yan Najeriya da su gaggauta kai rahoton bullar dabbobin da ke zubar da jini a jikinsu ga hukumomin kiwon lafiyar dabbobi ko kuma ma’aikatan aikin gona.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos