Cutar coronavirus ba mutuwa ba ce —Minista
Gwamanatin Tarayya ta ce duk da cewa cutar coronavirus ba tarkon mutuwa ba ce, illarta ga wadanda suka kamu ta isa ta zama izina ga ‘yan Najeriya kan su ci gaba da daukar matakan kariya. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya bayyana hakan yayin jawabin hadin gwiwa karo na 44 kan cutar coronavirus […]
Gwamanatin Tarayya ta ce duk da cewa cutar coronavirus ba tarkon mutuwa ba ce, illarta ga wadanda suka kamu ta isa ta zama izina ga ‘yan Najeriya kan su ci gaba da daukar matakan kariya.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya bayyana hakan yayin jawabin hadin gwiwa karo na 44 kan cutar coronavirus da Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya Kafa don Yaki da COVID-19 ya gabatar ranar Alhamis a Abuja.
A cewar ministan, ‘yan Najeriya da dama ba sa kiyaye ka’idoji da shawarwarin kan matakan kariya na yaki da cutar, yana mai cewa hanyar da kawai ‘yan Najeriya za su kare kansu ita ce bin shawarwarin Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da kuma kuma kwamitin na kar-ta-kwana ke bayarwa.
- An rufe Majalisar Dokokin Najeriya saboda fargabar coronavirus
- ‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’
“Ku yi addu’ar kada ku je asibiti, ku yi addu’ar kada ma cutar ta kama ku. Hanya daya ta kare kai ita ce sauraron shawarwarin masana. Mun sha nanata cewa har yanzu cutar nan ba ta da magani. Har yanzu ba a gano maganinta ba. Idan ma wani ya ce maka yana da maganinta to karya yak e yi”, inji ministan.
Lai Mohammed ya ce rigakafin cutar kawai a yanzu bai wuce bin sharuddan da hukumomin lafiya suka gindaya ba, kamar amfani da kyallen rufe fuska, bayar da tazara, guje wa shiga cunkoso, wanke hannu a kai a kai da kuma amfani da sinadarin tsaftace hannuwa.
“Babu wani magani baya ga wadannan matakan. Idan da kun san irin mawuyacin halin da wadanda suka kamu da cutar da ma wadanda yanzu suke dauke da ita su ke shiga, ba za ku taba so cutar ta kama ku ba.