Cutar Covid-19 ta sake harbin mutum 132 a Najeriya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar cewa cutar coronavirus ta sake harbin karin mutane 132 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin da daddare, 14 ga Satumban 2020. Allah Ya yi wa Sarkin Biu rasuwa Amurka ta haramta kayan China kan musguna wa […]

Cutar Covid-19 ta sake harbin mutum 132 a Najeriya

Shugaban Hukumar NCDC; Chukwemeka Ihekweazu

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar cewa cutar coronavirus ta sake harbin karin mutane 132 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin da daddare, 14 ga Satumban 2020.

A cikin sanarwar da hukumar ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na sada zumunta, ta ce an samu karin sabbin mutane 132 da suka fito daga jihohi 11 na Najeriya kamar haka:

Lagos (52),

Gombe (27),

Plateau (17),

Kwara (10),

Enugu (9),

Ogun (9),

Katsina (3),

Ekiti (2),

Bauchi (1),

Osun (1),

Ribas (1).