Cutar dajin mama na kashe mutum 700,000 duk shekara —Kwararru
Akalla mutum miliyan 2.3 ne ke dauke da cutar dajin mama
Akalla mutum miliyan 2.3 ne suke dauke da cutar dajin mama wadda kan yi ajalin mutum 700,000 a duk shekara a fadin duniya.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Daraktan Gidauniyar DHF, Dokta Ekundayo Samuel, a jawabinsa a wajen wani taro a Isanlu da ke Karamar Hukumar Yagba ta Gabas a Jihar Kogi.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram, Sun Ceto Matafiya A Borno
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ba Sa Tuhumar Shugabanni
Kwararren ya ce a halin yanzu cutar dajin mama shi ne nau’in cutar dajin da ke gaba da kowanne in banda cutar dajin huhu.
Ya ce a Najeriya kuwa, “A tsakanin shekaru biyar, lamarin ya kai matakin da da kyar mutum hudu cikin biyar masu dauke da cutar ke rayuwa.”
Ya kara da cewa, duk da cewa babu cikakken bayanin da aka tattara game da cutar, amma cutar dajin mama shi ne nau’in cutar dajin da ke kan gaba a Najeriya, kuma yakan yi ajalin mutane da daman gaske a duk shekara.
“Wannan shi ne dalilin da gidauniyarmu ta himmatu wajen lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen ba da kariya daga kamuwa da cutar da kuma yadda masu dauke da ita za su yi rayuwa,” in ji Dokta Samuel.