Cutar Diphtheria ta kama mutum 6 a Gombe
Cutar Diphtheria ta kama mutum 6 a Gombe
Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da cewa mutum Shida ne suka kamu da cutar ta mashako wato Diphtheria a Jihar.
Mataimakin likiti mai kula da cututtuka masu yaduwa na Asibitin Kwararru a Jihar, Dokta Israel James, ne ya shaida hakan ga wakilinmu yayin wani taro na yini biyu a Gombe.
- An soma taron jin kai kan Gaza a birnin Paris na kasar Faransa
- Gaza: Kungiyar kasashen Musulmi ta kira taron gaggawa
An shirya taron ne da hadin gwiwar ’yan jarida da masu ruwa da tsaki a tsakanin al’umma a kan cutar a Jihar.
Yace sun kira taron ne domin isar da sakon ga al’umma kan cutar kasancewar ’yan jarida na da muhimmiyar rawa waje isar da sako ga al’umma cikin kankanin lokaci.
Ya kara da cewa ana gane cutar ne ta hanyoyin mura da ciwon wuya da ke wahalar da mutane wajen hadiya da kuma kuraje a cikin baki da sauran alamomi.
Likitan ya ce ana ita kamuwa da cutar ta wajen shakar numfashi ko yin atishawa a cikin mutane da Kuma cudanyuwa da Juna.
Dokta Isreal, ya ce da zarar sun sami rahoton bullar cutar sukan ziyarci yankin domin su yi wa yara ’yan kasa da shekara 14 allurar rigakafi domin hana yadata ga wadanda ba su kamu ba.
Har ila yau, ya ce yaron da aka yi wa rigakafi tun yana karami ko da ya kamu da cutar bayan ya girma ba za ta yi tasiri a jikin sa ba.
Daga nan sai ya yi kira ga iyayen yara da su rika kai yaransu rigakafin domin samun kariya daga cututtuka.