Cutar diphtheria ta kashe mutane 40 a Kano
Akasarin wadanda cutar ta Diphtheria ta shafa kananan yara ne, kuma wasu da dama suna kwance a asibiti
Mutane 40 sun rasu, wasu da dama suna kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar numfashi ta diphtheria a Kano.
Rahotanni daga jihar na cewa akasarin wadanda cutar ta Diphtheria ta shafa kananan yara ne.
Aminiya ta ziyarci Asibitin Cututtuka Masu yaduwa (IDH) da ke Kano a ranar Laraba, inda ta iske dakuna uku cike da marasa majinyata da aka ba su gado, wasu kuma suna bin layin ganin likita.
Wani jami’in asibitin da ya nemi a boye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance, ya ce, kusan kullum sai an rasa rai a sakamakon cutar Diphyheria a asibitin.
- An ɗaure ‘yan Najeriya kan takardun auren bogi 2,000 a Birtaniya
- Abba ya rufe duk asusun ma’aikatun Kano
“Kusan mako biyu ke nan da cutar take kashe mutane, kuma kullum sai likitoci sun duba mutane kamar yadda kuke gani, jama’a na bin layi.
“Idan ka zo tun da sassafe za ka samu majinyata, haka ma da yamma. Daga lokacin da aka samu bullar cutar zuwa yanzu kullum marasa lafiya ake kawowa.”
A cewar jami’in, sauran asibitoci a karamar hukumar ba su da kayan duba masu cutar, don haka wasu marasa lafiyan ma daga wasu asibitocin ake dawo da su IDH.
Wata uwa mai suna Samira Danzaki wadda aka kwantar da ’yarta, ta ce sai da ta shafe kwana biyu kafin su samu ganin likita, amma a halin yanzu ’yar tana samun sauki.
Ita kuma wata wadda ke kan layin ganin likita, ta ce kwana biyu da suka wuce ta fara jin mura, amma daga bisani ta fara kasa nunfashi.
Mun tuntubi kakakin Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Sulaiman, kan lamarin, amma ba ta tabbatar ko musanta bullar cutar ba.
Sai dai amma ta ce suna gudanar da taron gaggawa kuma nan gaba a ranar Alhamis za su fitar da sanarwa.