Cutar Ebola
Wani Ibo ne mai ciwon kanjamau ya je asibiti don ganin likita. Saboda bullar wata sabuwar cuta mai suna Ebola, Ibo bai yarda ya gaisa da kowa ba. Duk wanda ya miko masa hannu sai ya kada kai, alamar yana amsawa. Ana nan har layi ya zo daga wata Bayarbiya sai shi. Daga cikin ofishin […]
Wani Ibo ne mai ciwon kanjamau ya je asibiti don ganin likita. Saboda bullar wata sabuwar cuta mai suna Ebola, Ibo bai yarda ya gaisa da kowa ba. Duk wanda ya miko masa hannu sai ya kada kai, alamar yana amsawa. Ana nan har layi ya zo daga wata Bayarbiya sai shi. Daga cikin ofishin likita da karfi aka kira sunan: “Bola.” Shi Ibo a tsammaninsa Ebola ake ce, kuma ana kiran mutum ne da sunan ciwon da yake da shi, sai ya yi wuf ya juya a guje, yana fadin “Chineke! I no touch Ebola o.” Yana nufin wai bai taba Ebola ba.
Daga Naseeru Taneemu Annuree (NTA), 08137284277