Cutar Ebola: Alhazan bana sun sha bincike a Saudiyya
Muhammad Yaba a Makka Alhazai daga Nahiyar Afirka musamman wadanda suka fito daga Najeriya, sun sha bincike a yayin da suka sauka a kasar Saudiyya don yin aikin Hajjin bana, domin a tabbatar babu wanda yake dauke da cutar Ebola.AbdulGhani Al-Maliki jami’in kasar Saudiyya da ke kula harkokin aikin Hajji a filin jirgin saman Sarki […]
Muhammad Yaba a Makka
Alhazai daga Nahiyar Afirka musamman wadanda suka fito daga Najeriya, sun sha bincike a yayin da suka sauka a kasar Saudiyya don yin aikin Hajjin bana, domin a tabbatar babu wanda yake dauke da cutar Ebola.
AbdulGhani Al-Maliki jami’in kasar Saudiyya da ke kula harkokin aikin Hajji a filin jirgin saman Sarki Abdul’Aziz da ke Jidda, ya ce an yi wa maniyyatan da suka fito daga Afirka, musamman Najeriya da Kenya da Kongo binciken kwakwaf, amma babu wanda aka samu da alamun cutar Ebola.
Ya ce, an samar da kwararrun likitoci a fannin cututtukan masu yaduwa domin gano masu dauke da cutar ta Ebola. Kuma an binciki maniyyatan da suka fito daga kowane bangare na duniya,’’ amma mun fi tsanantawa a kan maniyyatan da suka fito daga kasashen da aka samu rahoton bullar cutar, kamar Najeriya da Kenya da Kongo.’’
Wakilinmu ya ce, ana raba wa maniyyata wani fom domin a fahimci wurin da suke zaune kwanaki 21 kafin isarsu kasar Saudiyya, saboda kwanaki 21 cutar take yi kafin ta bayyana a jikin mutum.
Wani Minista a kasar Saudiyya Adel Fakeih ya ce ba a samu rahoton bullar wata muguwar cuta a tsakanin mahajjata sama da miliyan daya da rabi da suka isa kasar don gudanar da aikin Hajjin bana ba.
Jaridar kasar mai suna Arab News da ta ruwaito wannan bayanin, ta ce Ministan ya ce, “Jami’an kiwon lafiyarmu na kula tare da sanya ido a kan al’amuran da suka shafi kiwon lafiyar alhazanmu, cikinsu har da Sarki Abdallah.”
Mininstan Harkokin Aikin Hajji, Bandar Hajjar ya ce akalla alhazai miliyan 1 da dubu 360 sun isa Saudiya tun Lahadin makon jiya kuma suna sa ran za su ninka wannan adadi.
Jaridar ta ce, Hukumar Aikin Hajjin ta shirya wani taron bita mai taken: “Girmama Hurumomin Allah a Makkah,” domin bai wa malaman duniya damar tattaunawa su ilimantar da al’umma baki daya. Taron bitar na kwana uku, ya samu halartar masana da mawallafa da ’yan jarida daga kasashen duniya.
“Muna fatan za ku dauki dukkan bayanan da aka tattauna a wajen taron bitar zuwa kasashenku domin ilimantar da alhazanku,” inji Hajjar.
Hajjar ya ce, akwai bukatar a rika ilimantar da alhazai tun kafin su iso kasa Mai tsarki, “domin hakan zai taimaka wajen rage matsalolin da muke fama da su, ya taimaka wajen rage kura-kuran da alhazai ke tafkawa wajen aikin Hajji,” inji shi
A jawabin, babban limamin Masallacin Ka’aba, Sheikh Abdul Aziz Al-Asheikh ya ce mutunta aikin Hajji kamar mutunta Allah ne, don haka ya ce taron zai taimaka wajen dora alhazai a kan turba madaidaiciya.
Ya yaba wa gwamnatin kasar kan kokarin da take yi na fadada masallacin Ka’aba, domin hakan zai taimaka wajen rage cinkoson jama’a.
“Musulman duniya na fuskantar kalubale saboda rabuwar kawuna saboda haka muna kira ga Muslumi su hada kai a kan Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah da yin ayyuka masu kyau,” inji limamin.
Ya nemi a janyo hankalin matasa Musulmi tare da kare su daga shiga kungiyoyin ’yan ta’adda.
Hisham bin Abdullah Al-Abbas, Sakatare-Janar na taron bitar, ya ce taron zai taimaka wajen hana alhazai yin wasu ayyuka da ka iya bata musu Hajji, kuma za su fahimci cewa haramun ne alhaji ya cutar da alhaji dan uwansa.