Cutar Ebola: Hukumomin Alhazai sun dauki mataki

A sakamakon bullar cutar Ebola a wani yanki na kasar nan, cikin maniyyata aikin hajjin bana ya duri ruwa, musamman da suka ji cewa kasar Saudiyya ta hana maniyyatan kasashen Saliyo da Guinea da kuma Liberiya da cutar ta yi kamari zuwa aikin hajji da umura har sai abin da hali ya yi.Hukumomin kasar Saudiyya […]

Cutar Ebola: Hukumomin Alhazai sun dauki mataki

A sakamakon bullar cutar Ebola a wani yanki na kasar nan, cikin maniyyata aikin hajjin bana ya duri ruwa, musamman da suka ji cewa kasar Saudiyya ta hana maniyyatan kasashen Saliyo da Guinea da kuma Liberiya da cutar ta yi kamari zuwa aikin hajji da umura har sai abin da hali ya yi.
Hukumomin kasar Saudiyya dai sun ce saboda bullar cutar duk wani maniyyaci da zai shiga kasarsu sai an tabbatar da koshin lafiyarsa kafin a bar shi ya shiga kasar.
Sai dai kuma hukumomi a Najeriya ba su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cutar ba ta bazu wadansu yankunan na kasar nan ba, inda suka himmatu wajen ganin cewa cutar ta takaita ne a Legas kawai, watau wurin da Mista Patrick Sawyer da ya shigo da cutar daga kasar Liberiya ya sauka.
Hukumar alhazai ta kasa da sauran hukumomin alhazai na jihohi sun bayyana cewa sun dauki kwararan matakai domin ganin cutar ba ta shafi wani maniyyaci daga kasar nan ba.
A cewar Uba Mana, kakakin hukumar alhazai ta kasa, hukumar tasu ta umarci hukumomin alhazai da ke jihohin kasar nan su tabbatar sun tantance kowane maniyyaci a yayin da ya isa sansanin alhazai kafin ya tashi zuwa kasa mai tsarki. Yana mai gargadin cewa ba za a bar duk wanda aka ga yana da alamar cutar a tare da shi ya fita kasar nan ba, kuma idan aka samu wani alhaji ya kamu da cutar a kasa mai tsarki ba za a bar shi ya dawo gida ba, sai ya warke.
 Shi ma Kwamishinan Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON), mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma,  Alhaji Salisu Ado Shinkafi, ya bayyana shirin da hukumar jin dadin Alhazai ta kasa take yi dangane da cutar Ebola, inda ya ce, “Hukumar NAHCON tana iyakar kokarinta wajen ganin ta fadakar da maniyyata  irin matakan da aka dauka domin kare su daga wannan cutar.
“Za mu cigaba da fadakar da su har zuwa lokacin tashi  a kullum yadda za su kare kansu. Wadannan ka’idoji da jami’an asibiti suka fadi ne za a cigaba da fada wa jama’a, domin mu ba masana ba ne a fannin aikin kiwon lafiya. Amma idan an fadi mana mu fada, za mu yi kokari mu fada domin cigaban al’ummarmu,” inji shi.
Daga Jihar Sakkwato kuma wakilinmu Nasiru Bello ya ruwaito Alhaji Faruku Umar, mai taimaka wa hukumar jin dadin alhazai ta jihar kan harkokin yada labarai  kuma sakataren karamin kwamitin wayar da kan alhazai yana cewa,  “Hukumarmu ta jin dadin alhazai, karkashin jagorancin Alhaji Muntari Mai gona ta dauki duk wani matakin da ya dace domin wayar da kan maniyyatan Jihar Sakkwato domin su kare kansu daga kamuwa da wannan cutar ta Ebola. A yau da kake magana da ni mun fara zagaye a kananan hukumominmu 23 don wayar da kansu domin su san mene ne wannnan kwayar cutar; me ke kawo ta; ya mutum zai yi ya kare kansa daga kamuwa da wannan cutar? Da sauran bayanai da suka shafi kiwon lafiya.”
Ya kara da cewa, “Ka san wannan cutar har yanzu ba ta zo gefenmu ba, amma duk da haka a kowace karamar hukuma da muka je tare da jami’an lafiya muke zuwa domin yin gwaji ga kowane Alhaji da Hajiya don tantance su, da zarar muka samu mai wata babbar matsalar ciwo, kamar tari ko juna biyu da sauransu, za mu hana shi zuwa tare da maye gurbinsa.”
Alhaji Faruku, wanda ya yi wa wakilinmu wannan bayanin ta waya, ya ci gaba da cewa, “Yanzu haka hukumar ta samo na’urar gwaji da ake amfani da ita domin tantace masu wannan cutar, wadda za su yi aiki da ita, babu wani maniyyaci a Jihar Sakkwato da zai shiga jirgi sai mun tantance lafiyarsa, duk wanda muka samu da wani zazzabi da aka kasa ganewa, za mu hana shi shiga jirgi, har sai ma’aikatan lafiya sun yi binciken kwakwaf a kansa. Da haka nake son fada maka cewa duk wani shiri na samun nasara muna aiwatar da shi ga maniyyatanmu, za  mu kuma cigaba da yi har lokacin da aka kammala aikin hajji muka dawo gida Najeriya. Mun dauki matakin da ya kamata ga mahajjatanmu kan cutar Ebola.”  
Daga Kaduna kuma wakilinmu Muhammad Yaba, ya ruwaito cewa, Hukumar Jin dadin Alhazai na jihar ta shirya tsaf dangane da kula da lafiyar alhazanta tun daga nan gida zuwa kasa mai tsarki.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Yunusa Muhammad Abdullahi ne ya bayyana haka, inda ya yi nuni da cewa, kamar kowace shekara, hukumar tana mayar da hankali sosai kan batun kiwon lafiyar alhazan jihar, don haka a wannan shekarar ma ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ba su takardu domin su je asibitin gwamnati a duba lafiyarsu tun kafin a soma tashi zuwa kasar Saudiyya.
“Tuni muka bai wa dukkan alhazanmu fom domin su je asibiti a duba lafiyarsu, watau (tes), tun kafin a fara tashi zuwa Saudiyya. Mata kuma dole sai an duba su ko suna da juna biyu, da dai makamantarsu,” inji shi.
Har ila yau Malam Yunusa ya bayyana cewa, kafin a kammala tantance kowane Alhaji ko Hajiya, sai ta sake yin wani gwaji a sansanin Alhazai, “Duk muna yin hakan ne domin tabbatar da lafiyarsu.”
 Haka kuma wata jami’ar lafiya a Ma’aikatar  Lafiya ta Jihar Kaduna, Hajiya Zainab Umar ta bayyana a  wajen wani taron masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji da aka yi a Hukumar Jin Dadin Alhazan jihar, a makon jiya, cewa gwamnatin jihar tana sane da kalubale da cutar Ebola ke neman janyo wa kasar nan, saboda haka tuni ma’aikatar lafiya da yardar gwamnatin jihar ta samar da sashe na musamman domin kebe duk wani Alhaji ko Hajiya da za a samu da alamun cutar  Ebola a filin jirgin sama.
A cewarta, gwamnati ta damu da bullar cutar a Jihar Legas, duk kuwa da cewa ba a samu bullar cutar a Jihar Kaduna ba.
Daga Jihar Legas kuwa, inda cutar Ebola ta bulla a kasar nan, wakilinmu Abubakar Ibrahim ya ruwaito cewa, Hukumar  Alhazai  ta  jihar  ta ce  a  halin  yanzu  ba ta  da  wani  shiri  na  musammam  game  da  cutar  Ebola  ga  alhazanta,  sai  wanda  gwamnatin  tarayya  ta  tsara, za ta yi wani abu ne kawai  idan  tsarin  gwamnatin tarayya  bai  kai  ga  tasarin  da  take  jin ya  dace  ba.
Mai  magana  da  yawun  hukumar  alhazai  na  jihar, Mista  Durojaye   ya ce  kodayake  wannan  batu  ne  na  ma’aikar kiwon  lafiya,  su  nasu  isar  da umurni ne,  amma  dai  a halin  yanzu  babu  wani  tsari ko  shiri  da  za a ce  an  yi  da  ya  bambanta  da na  sauran  jihohi.
Ya ce  amma  da  zarar  ma’aikatar  kiwon  lafiya  ta  jihar  ta  fidda  wani  tsari   ko  kuma  umurni,  su kuma  hukumar  alhazai  ba su  da  zabi. Ya ce  sun kammala  nasu shirin game  da  gudanar  da  aikin  hajji   na  wannan  shekarar,  ba  wani  abu  da  ya  rage.
   A Jihar Neja kuwa wakilinmu Muhammad danladi Ibrahim  ya ruwaito cewa, Sakataren Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai na Jihar Neja, Sheikh Musa Ibrahim ya ce sun dauki matakan da suka hada da wayar wa maniyyata kai ta kafafen watsa labarai da suke fadin jihar.
Sakataren ya ce hukumarsu tana da kwararrun likitocin da ke wayar wa maniyyata kai duk shekara, musamman wadanda za su tashi ta Jihar Neja, game da hanyoyin da ake bi domin kamuwa da cuta, don haka wannan ba sabon abu ba ne a gare su.
Ya ce akwai cibiyoyin tantance jama’a da gwamnatin jihar ta bude guda uku a dukkan shiyyoyin Majalisar Dattawa domin auna wadanda aka gansu da alamun wannan cutar, da suka hada da zazzabi mai tsanani da amai da gudawa, sai zubar jini ta baki da kunnuwa da hanci. Ya ce wadanda suka fi saurin kamuwa da cutar sun hada da masu cin beraye da birai da jemage da alade.
Sai ya shawarci jama’a da su gaggauta zuwa wurin likita a duk lokacin suka ji alamun zazzabi mai tsanani a jikinsu. Ya ce daukar wannan matakin zai taimaka wurin gano hanyoyin da za a yi saurin shawo kan lamarin. Kuma ya kamata su rungumi akidar tsaftace jiki da muhalli kamar yadda Annabi Muhammad [S.A.W.] ya koyar.
A Jihar Yobe kuma wakilinmu Sani Gazas Chinade ya ruwaito cewa Sakataren hukumar alhazai na jihar,  Alhaji  Bukar  Kime ya bayyana cewa hukumarsu tuni ta dauki matakin ilmantar da maniyyatan jihar dangane da cutar Ebola.
Sakataren ya ce sun dauko kwararren likita don ilmantar da maniyyatan dangane da alamomi da kuma illar cutar ta Ebola. Kuma za su cigaba da daukar wannan matakin nasu har sai sun ga komai ya yi daidai.
Daga Kano kuma, jihar da ta fi yawan maniyyata a Najeriya, wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Sakataren hukumar alhazan jihar, amma aka ce ya yi tafiya, shi kuma Jami’in hulda da jama’a ya ce ba zai ce komi ba dangane da batun cutar Ebola, sai dai ma’aikatar lafiya. Da wakilinmu ya nufi ma’aikatar lafiyar, bai yi sa’ar samun wani bayani ba.
A waje  daya  kuma,  daya  daga  cikin likitocin  nan da  suka  kamu  da  cutar  ta  Ebola,  sakamakon  yi wa  dan  kasar  Liberiyan  nan  magani  ta  rasu  cikin dare  ranar  Talata  a  birnin  Ikko a  inda  aka  kebe  su  ana yi  musu  magani.
Likitan, mai suna  Ameyo  Stella  Adedayo,  tana  sahun  farko  cikin  likitocin  da  suka  duba  Mista Patrick Sawyer,  a  wani asibiti  mai   zaman kansa  da ke  unguwar  Obalende  a  cikin birnin Ikko. Bayanai sun nuna cewa  ita  dai  wannan baiwar  Allah  da  ta  rasu,  tana  da  sama  da  shekaru  55,  tana  cikin  manyan  likitocin  asibitin  da  aka  kai Mista Sawyer  jinya. Kuma a lokacin da aka kai Mista Sawyer asibitin ba ta aiki, tana gida aka kira ta domin ta taimaka wajen ceto ran majinyacin, ashe shi ne zai zama sanadiyyar  rasuwarta.
A halin yanzu  dai adadin  wadanda  suka  mutu  sakamakon  wannan cutar  sun kai  biyar  ke nan  a Najeriya, a yayin da kuma  mutane biyar  suka  warke, inda  likitoci  suka tabbatar  ba su  dauke  da kwayar  cutar.