Cutar Ebola kalubale ne ga duniya – Hukumar WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, barkewar cutar Ebola mai saurin kisa a Yammacin Afirka shi ne babban kalubale ta fuskar kiwon lafiya da ta taba fuskanta a daidai lokacin da bayanai suke nuna cutar ta hallaka fiye da mutum 100 a kasar Guinea.Mataimakin shugabar huku-mar, Keiji Fakuda ya yi kashedin cewa, za a […]
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, barkewar cutar Ebola mai saurin kisa a Yammacin Afirka shi ne babban kalubale ta fuskar kiwon lafiya da ta taba fuskanta a daidai lokacin da bayanai suke nuna cutar ta hallaka fiye da mutum 100 a kasar Guinea.
Mataimakin shugabar huku-mar, Keiji Fakuda ya yi kashedin cewa, za a kwashe tsawon wata hudu nan gaba kafin a ci karfin cutar.
Ya ce, “Yana da muhimman-cin gaske a dauki matakin wayar da kan jama’ar da wannan cuta ta shafa, domin jama’a su samu cikakkun bayanai a kanta.”
Zuwa yanzu cutar ta Ebola ta kashe akalla mutum 101 a kasar Guinea da mutum 10 a kasar Liberiya.
Cutar ta Ebola tana yaduwa ne ta hanyar cudanya da msu dauke da ita, kuma tana kashe kashi 25 zuwa 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita.
kasashe da dama da ke makwabtaka da kasar Guinea sun rufe iyakokinsu da ita sakamakon bullar cutar, yayin da kasar Saudiyya ta haramta wa mutanen kasashen Guinea da Liberiya zuwa aikin Hajjin bana.
A watan jiya ne aka bayar da rahoton fara bayyana cutar a Kudancin Guinea kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Keija Fukuda, ya shaida wa taron manema labarai a Geneba cewa Hukumar WHO ta samu bayanan da ke zargin cewa mutum 157 cutar ta harba a Guinea ciki har da mutum 20 a Conakry babban birnin kasar. Sai dai ta tabbatar da cewa mutum 67 tabbas cutar ce ta kama su.
A Liberiya an samu bayanin mutum 21 sun kamu da cutar, sai dai biyar ne kawai aka tabbatar cewa cutar Ebola ce.
Wannan ne karo na farko da ake da hakikanin bayanin cutar Ebola ta bayyana a kasar Guinea – wadda ke nisan dubban mila-milai daga Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da Uganda. Kuma cutar ba ta da magani ko rigakafi.
kwayoyin cutar dai suna haifar da mummunan zazzabi da ke jawo ciwon baya da gajiya da amai da gudawa da zubar jini ba kakkautawa.