‘Cutar Ebola na barazana ga Birtaniya’

A shekaranjiya Laraba ne Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Philip Hammond ya ce gwamnatin kasar na nazarin annobar Ebola da ta barke a yankin Yammacin Afirka, a matsayin wata babbar barazana ga kasarta.Mista Hammond ya yi wani zama da babban kwamitin harkar tsaro don tattaunawa a kan annobar.kungiyar Tarayyar Turai dai ta kebe Dala miliyan biyu […]

‘Cutar Ebola na barazana ga Birtaniya’
‘Cutar Ebola na barazana ga Birtaniya’

A shekaranjiya Laraba ne Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Philip Hammond ya ce gwamnatin kasar na nazarin annobar Ebola da ta barke a yankin Yammacin Afirka, a matsayin wata babbar barazana ga kasarta.
Mista Hammond ya yi wani zama da babban kwamitin harkar tsaro don tattaunawa a kan annobar.
kungiyar Tarayyar Turai dai ta kebe Dala miliyan biyu da dubu dari bakwai don taimakawa wajen yaki da cutar.
Sai dai yayin da kasashen duniya da dama ke kokarin daukan matakan kariya, ciki har da yunkurin rufe iyakokinsu, kungiyar agajin likitoci ta ‘Doctor Without Borders’ ta ce rufe mashigun kasashen ya fi barinsu a bude hadari.
Sandra Smiley jami’a ce a kungiyar ta kuma bayyana wa kafar yada labarai ta BBC cewa: “Hana zirga-zirga mutane zai  maida yaki da wannan annobar baya, saboda wasu za su koma neman barauniyar hanya, inda kuma za a sha wahalar gaske wajen sa ido hakan.”
A karshen makon jiya ne dai wani dan Liberiya ya rasa ransa sanadiyyar cutar a wani asibiti da ke jihar Legas bayan ya shigo Najeriya daga Liberiyan. Tun bayan faruwar wannan lamarin ne hukumi suka fara daukar matakan kiyaye bullar cutar a Najeriya.
Hakazalika, hukumomin a kasar Laberiya sun rufe hanyoyin shiga kasar domin dakatar da bazuwar cutar wadda take saurin halaka jama’a. A makwabciyyarta Sierra Leone kuwa, a ranar Talata ne cutar ta yi ajalin likitan nan da ke jagorantar yaki da ita a kasar, Dokta Sheikh Umar Khan kwanaki kadan bayan harbuwarsa da cutar.
Mutane fiye da 670 ne suka rasu a kasashe ukun da ke fama da annobar wato: Guinea da Sierra Leone da kuma Laberiya tun bayan bullarta a watan Fabrairun bana.