Cutar Ebola na barazana ga kasashen Yammacin Afirka
Rahotanni sun tabbatar da bullar cutar Ebola a Liberia bayan barkewar ta a kasar Guinea mai makwabtaka da ita daga kudu, inda a can aka tabbatar da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 78.daya daga cikin wadanda suka harbu da cutar a kasar ta Liberia dai bai jima da dawo daga kasar Guinea ba, inda […]
Rahotanni sun tabbatar da bullar cutar Ebola a Liberia bayan barkewar ta a kasar Guinea mai makwabtaka da ita daga kudu, inda a can aka tabbatar da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 78.
daya daga cikin wadanda suka harbu da cutar a kasar ta Liberia dai bai jima da dawo daga kasar Guinea ba, inda akai amannar daga can ne ya dauko kwayar cutar. Dalili da yadda cutar ke ci gaba da yaduwa ne kuma, kasar Senegal ita mai makwabtaka da Guinea ta rufe dukkannin iyakokinta da kasar Guinea.
A wani mataki da kasar Saudiyya ita ma ta dauka don kiyaye yaduwar cutar a duniya, hukumomin kasar sun ce, ba za su ba da bizar zuwa aikin Hajjin bana ba ga maniyyatan kasashen Guinea da kuma Liberia saboda barkewar cutar Ebola a wadannan kasashen.
Mutum na iya harbuwa ne da cutar ta Ebola ta hanyar yin mu’amala da wanda ke dauke da ita kuma cutar na kisan kashi tara cikin goma na wadanda suka harbu da ita.
Bugu da kari, shahararran mawakin nan dan kasar Senegal Youssou Ndour ya soke wani bikin kalankuwa da ya shirya gabatarwa ranar Asabar da ta gabata a kasar ta Guinea, dalili da barkewar cutar. Duk da cewa ya isa babban birnin kasar Conakry, amma ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC dalilinsa inda ya ce “a cikin wannan yanayin annubar cutar Ebola da aka shiga a kasar Guinea, bai dace ba ce an tara dubbannin mutane a guri guda dalili da yadda cutar ke da saurin yaduwa” Inji shi
Cutar ta fara barkewa ne a kasar ta Guinea cikin watan Janairu a wani gari mai nisa da ke yankin kurmin Kudu-maso-Gabas na kasar. Daga nan ne sai ta ci gaba da bulla sassa daban-daban na kasar, inda a makon jiya ta isa babban birnin kasar, Conakry.
Ana gane mutum ya harbu da cutar ne idan aka ga alamomi kamar su: zazzabi mai tsanani da ciwon gabobin jiki da kasalar jiki da hararwa da kuma gudawa. Har-ila-yau idan cutar ta ci karfin jiki, za ta iya haifar da tsayawar wasu daga cikin sassan jiki da kuma yoyan jini.