Cutar Ebola na ci gaba da barazana a Yammacin Afirka

kungiyar Agaji ta Likitoti wato (Doctors without Borders) ta ce idan hukumomin duniya ba su taimaka wajen yakar cutar Ebola da ke barazana a yankin Yammacin Afirka ba, annobar za ta ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya.Daraktan Tsare-Tsaren din kungiyar Bart Janssens ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na (AP). Inda […]

Cutar Ebola na ci gaba da barazana a Yammacin Afirka
Cutar Ebola na ci gaba da barazana a Yammacin Afirka

kungiyar Agaji ta Likitoti wato (Doctors without Borders) ta ce idan hukumomin duniya ba su taimaka wajen yakar cutar Ebola da ke barazana a yankin Yammacin Afirka ba, annobar za ta ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya.
Daraktan Tsare-Tsaren din kungiyar Bart Janssens ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na (AP). Inda ya ce karfin kungiyar ya fara karewa kan game da aikin agajin da take samar wa a kasahen da annobar ta barke. Kuma y ace akwai bukatar aiki sosai idan ana so a ga bayan cutar a duniya.  
Ya ce: “Abun da yake a zahiri shi ne cutar na ci gaba da yaduwa. Kuma a yanzu za a iya cewa ta zama wata annoba.”
Cutar ta fara barkewa ne a kasar Guinea a farkon wannan shekarar. A watannin da suka gabata an zaci cutar ta kwanta kafin labarin bullarta a kasar Liberiya mai makwabtaka da Guinea.   
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa akalla mutum 330 suka mutu a kasashen Guinea da Sierra Leone da kuma Liberiya sanadiyyar kamuwa da kwayar cutar.
Mai Magana da yawun hukumar WHO ya ce dalili da yadda cutar take ci gaba da yaduwa cikin sauri a kasashe da dama, hakan ya sa ta zama annobar Ebola ma fi muni da aka taba gani a tarihin duniya.
Ya ce annobar ba ta da alamar tsayawa kuma ba wata alama da ke nuni da cewa an samu galaba a kanta. Hukumar ta ce ya dace kasahen duniya su ta shi tsaye don yakar ta. “Idan kuma ba a samu haka ba, to za ta ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.” Inji hukumar.