Cutar Ebola ta ci gaba da zama alakakai a Guinea
kasar Guinea tana daga cikin kasashen da annobar Ebola ta yi kamari kuma hakan ya sanya baki da ’yan yawon bude ido kaurace wa kasar, kamar yadda wasu mazauna kasar suka bayyana wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa harkokin kasuwanci sun tsaya cik a duk fadin kasar.A Conakry, babban birnin kasar, wani mutum mai […]
kasar Guinea tana daga cikin kasashen da annobar Ebola ta yi kamari kuma hakan ya sanya baki da ’yan yawon bude ido kaurace wa kasar, kamar yadda wasu mazauna kasar suka bayyana wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa harkokin kasuwanci sun tsaya cik a duk fadin kasar.
A Conakry, babban birnin kasar, wani mutum mai suna Issouf Balde ya shaida wa kafar yada labarai ta Aljazeera cewa: “Ina gab da samun cika burina na sauke farali a bana, amma sai ga wannan annobar ta kunno kai. Wanda hakan ya sa mahukuntan kasar Saudiyya suka ce ba za su ba da izinin zuwa aikin hajji ba ga duk wani maniyyaci daga kasar.”
Ya ci gaba da cewa sakamakon annobar ya sa an dawo masa da kudin da ya biya saboda matakin na Saudiyya. “Idan ba an kawo karshen wannan annobar ba ne, Saudiyya ba za ta bai wa mahajjatan Guinea izinin sauke farali ba a bana. Ka ga da wannan an rusa mani lissafina ke nan. Amma babbar damuwa ta ita ce wata kila wannan ne karon farko kuma na karshe saboda yadda nake da shekara 62 yanzu, da wuya na iya tara wasu kudin don zuwa aikin hajji anan gaba,” inji shi.
Bugu da kari Hukumar da ke Kula da Harkokin kwallon kafa a nahiyar Afirka (CAF) ta ba da umarnin cewa tawagar ’yan wasan kwallon kafar kasar ba za ta buga wasannin share fagen shiga Gasar Cin Kofin kwallon kafa na kasashen Afirka ba a gida, wanda za a fara gudanarwa cikin watan gobe. Hukumar ta ba da wannan umarnin ne saboda tsoron barazanar yaduwar cutar a lokacin da ake gudanar da wasannin.
Tun bayan da kasar ta dawo kan turbar dimukradiyya a karshen shekarar 2010, a duk shekara, Guinea tana samun baki ’yan yawan bude ido da suka shigowa kasar wadanda za su kai dubu 130, kamar yadda ma’aikatar da ke kula da ayyukan yawon bude ido ta bayyana. Amma a bana a ganin hakan zai samu mummunar koma-baya.