Cutar Ebola ta kashe mutum 4 a Sierra Leone
ukumomi a kasar Sierra Leone sun tabbatar da mutuwar mutum hudu bayan barkewar annobar cutar Ebola a kasar. Ma’aikatar Lafiyar kasar ta bayyana cewa cutar ta barke ne a garin Kailahum da ke yankin gabacin kasar, wanda kuma yake makwabtaka da yammacin kasar Guinea. Inda daga nan ne annobar ta fara a cikin watan Maris, […]
ukumomi a kasar Sierra Leone sun tabbatar da mutuwar mutum hudu bayan barkewar annobar cutar Ebola a kasar.
Ma’aikatar Lafiyar kasar ta bayyana cewa cutar ta barke ne a garin Kailahum da ke yankin gabacin kasar, wanda kuma yake makwabtaka da yammacin kasar Guinea. Inda daga nan ne annobar ta fara a cikin watan Maris, wanda kuma ta kashe mutane akalla 145 a can. A kasar Liberiya ma, an samu rahotan mutuwar mutum tara sanadiyyar kamuwa da cutar.
Daraktar Ma’aikatar Lafiyar Sierra Leone, Dokta Amara Jambai ya ce cikin mutum hudu da suka rasa rayukansu a kasar akwai ma’aikatan jinya a ciki. Ma’aikatar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta fara aikawa da magunguna kasar a kokarinta na shawo kan cutar.
Masana ciwon lafiya sun ce cutar ba ta da magani, ko rigakafi. Kuma daya ce cikin cututtuka masu saurin kisa da kuma yaduwa. Amma ana iya shawo kanta idan aka tare da magani a farkon lokacin da aka harbu da ita. kwayar cutar na iya kashe mutum tara cikin goma daga cikin wadanda suka kamu da ita. Ana kamuwa da ita ne ta hanyar mu’amala da bawali, ko jibi, ko kuma jinin dabbar, ko mutumin da ya harbu da ita. Jinsin jemage da ke bibiyan ’ya’yan itatuwa ne babban mai yada ta. Zazzabi mai zafi da kuma yoyon jini, su ne manyan alamomin wanda ya harbu da ita.