Cutar Ebola ta zama alakakai
Cutar Ebola ta zama alakakai ga wadansu kasashe da ke yankin Afirka ta Yamma ciki har da Najeriya sakamakon yadda aka fara mayar da su saniyar ware a tsakankanin kasashen duniya.Ministan lafiya Farfesa Onyenbuchi Chukwu kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar, domin haka wata cibiyar daukar matakan gaggawa na […]


Cutar Ebola ta zama alakakai ga wadansu kasashe da ke yankin Afirka ta Yamma ciki har da Najeriya sakamakon yadda aka fara mayar da su saniyar ware a tsakankanin kasashen duniya.
Ministan lafiya Farfesa Onyenbuchi Chukwu kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar, domin haka wata cibiyar daukar matakan gaggawa na hana bazuwar cutar ta fara aiki a jihar Legas daga jiya Alhamis, ba dare ba rana.
Annobar wadda zuwa yanzu ta hallaka kusan mutum 900, ta sa wadansu kasashen duniya da dama sun fara daukar matakan kiyaye bullarta cikin kasashensu. Wannan ya sa a ranar Talata mahukunta a kasar Ghana suka haramta wa ’yan Najeriya da sauran ’yan kasashen ’yankin izinin shiga kasar. Hakazalika, kasar Saudiyya ta bayyana haramta wa wadansu kasashen yankin Afirka ta yamma uku (Laberiya da Guinea da Saliyo) izinin zuwa aikin Hajjin bana, sakamakon barkewar cutar mai saurin kisa a kasashensu.
Cutar mai saurin yaduwa ta fara bulla ne kimanin shekara 38 da suka wuce a tsohuwar kasar Zaire, wato Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo a yanzu. Inda daga can ne aka rada mata sunan Ebola, wanda ya samo asali daga sunan wani rafi a garin da cutar ta fara bulla a wancan lokacin. Kodayake a watan Fabrairun bana ne kwayar cutar ta kara bulla, amma wannan karon a kasar Guinea wadda take yankin Yammacin Afirka, inda daga nan ne ta ci gaba da yaduwa zuwa kasashen Saliyo da Laberiya da kuma Najeriya.
Kodayake an tabbatar da cewa kwayar cutar ta shigo kasar nan ne bayan da wani dan Laberiya, mai suna Patrick Sawyer ya rasu a karshen watan jiya sanadiyyar cutar a wani asibiti da ke unguwar Obalende ta jihar Legas. An yi amannar cewa marigayin ya dauko kwayar cutar ne daga kasar Laberiya bayan wata ziyara da ya kai can, kwana biyar kafin rasuwarsa. Har ila yau, a makon jiya ne mazauna jihar Anambra suka shiga zaman fargabar bullar annobar bayan wadansu rahotonni da ke cewa an shigo da wata gawa jihar daga Laberiya wadda aka yi amannar cutar ce ta yi ajalinta.
A ranar Litinin da ta gabata ne kuma Ministan Kiwon Lafiya Farfesa Onyebuchi Chukwu ya tabbatar da cewa likitar da ta duba Mista Patrick a jihar Legas, ta kamu da cutar. Ministan ya ce ana can ana yi mata magani, kuma a yanzu mutane 70 da aka tabbatar cewa sun yi mu’amala da mamacin, ana kula da su, inda takwas daga cikinsu aka kebe su. An kuma dauki jinin karin wadansu mutum uku da alamu suka nuna suna dauke da kwayar cutar, domin yin gwaji.
Sai dai kuma a shekaranjiya laraba minista a ma’aikatar lafiya ya sanar da manema labarai bayan an kammala taron majalisar zartarwaa Abuja cewa wata ma’aikaciyar jinya da ta duba dan kasar Laberiyan ita ma ta rasu, inda ta zama ‘yar Najeriya ta farko da ta rasa ranta a sakamakon cutar, kuma hakan ya sanya aka samu mutane biyu da cutar ta halaka a Najeriya.
A karshen makon jiya ne kuma kamfanin jiragen sama na Emirates ya dakatar da jigila zuwa kasar Guinea har sai abin da hali ya yi saboda annobar. A cikin wata sanarwa a shafinsa na Intanet, kamfanin ya ce ba zai yi sakaci da lafiyar fasinjojinsa da ma’aikatansa ba. Hakazalika wadansu kamfanonin jiragen sama da suka hada da Arik Air da ASky na kasar Togo sun dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa kasashen da cutar ta bulla.
A ci gaba da daukar matakan yaki da bullar cutar, a ranar Litinin ne kasar Koriya ta Kudu ta janye gayyatar da ta yi wa wadansu ’yan Najeriya uku don halartar wani babban taro kan ilimin mata da wata jami’ar kasar ta shirya da hadin gwiwar Majalisar dinkin Duniya.
Ita ma kasar Saudiyya a wani mataki na kandagarki, ta fitar da sunayen kasashe da ba za a ba ’yan kasarsu izinin aikin Hajjin bana ba saboda bullar annobar a kasashen da suka fito. kasashen kuwa su ne Guinea da Saliyo da kuma Laberiya. Hukumomin kasar sun kuma bayyana cewa, dan dasar wanda ya kamu da cutar sakamakon ziyarar da kai kasar Saliyo. ya rasu. Kodayake har zuwa wannan lokacin, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta kai ga ba da umarni a hukumance ba kan takaita zirga-zirgar jama’a ko rufe iyakokin kasashen da annobar ta yi kamari ba. Amma hukumar ta ce cikin mutum dubu daya da 603 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar zuwa yanzu, akwai ’yan Najeriya mutum hudu a ciki.
Ana gane mutumin da ya harbu da cutar ne idan aka ga alamomi kamar su: zazzabi mai tsanani da ciwon gabobin jiki da kasalar jiki da hararwa da kuma gudawa. Har ila yau idan cutar ta ci karfin jiki, tana iya haifar da tsayawar wadansu daga cikin sassan jiki da kuma yoyan jini.
An kama hanyar shawo kan matsalar
Amma duk da cewa da farko masana sun bayyana cewa cutar Ebolar ba ta da rigakafi, ko magani. A yanzu an kama hanyar shawo kanta, inda kwararru a fannin kiwon lafiya suka ce idan aka gane cutar da wuri kuma aka tare ta da magani akwai yuhuwar za a iya samun waraka. Saboda a yanzu haka akwai likitocin Amurka biyu Dokta Kent Brantly da kuma Dokta Nancy Writebol da aka ce sun fara murmurewa daga cutar bayan da suka kamu da ita a lokacin da suke aikin bai wa wadansu da ke dauke da kwayar cutar kulawa a kasar Laberiya. A karshen makon jiya ne aka koma da likitocin Amurka inda aka nufi wani asibiti da ke birnin Alaska da su. Hakazalika, akwai wani rahoton da ya fito daga kasar Guine da ya ruwaito cewa daya daga cikin likitocin kasar da ke fama da cutar, ya warke.
Bugu da kari akwai kamfanin hada magunguna na Mapp Biopharmaceutical Inc. da ya ce ya kirkiri wani maganin cutar mai suna Zmapp, wanda ya kawo waraka lokacin da aka gwada shi a jikin birrai. Kuma wadansu manasa sun bayyana cewa kwayoyin maganin ne ake ci gaba da gwadawa a jikin likitocin nan na Amurkawa da ke murmurewa daga cutar a halin yanzu.
Wannan ya sa a shekaranjiya Laraba, ministan lafiya Farfesa Chukwu ya kira wani taron manema labarai, inda ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta tuntubi Cibiyar Kiyaye Yaduwar Cututtuka ta kasar Amurka don ganin yadd za a samar da maganin a nan Najeriya. Har ila yau, kungiyar likitoci ta kasa wadda membobinta suke cikin yajin aiki, ta bayyana kafa wani kwamiti wanda zai jagoranci yaki da bazuwar cutar da kuma aikin wayarwa da al’umma kai.
Kada a yarda da masu cewa suna da maganinta -Dokta Sani Gwarzo
Abubakar Ibrahim a Legas
Shugaban yaki da cutar ebola Dokta Nasir Sani Gwarzo ya shaida wa Aminiya cewa gwamnatocin jihohi tarayya sun hada hannu domin hana wannan cutar bazuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Dokta, da yake dan kkasar Liberiyan nan da cutar ta kashe ta jirgi ya shigo Najeriya, to su kuma sauran wuraren da ake shigowa cikin kasar wadanne matakai kuke dauka game da su,?
Gwarzo: Mun fara aiki a ire-iren wadannan bakin iyakokin da muke da ire-iren su sun kai 200, kuma mun fara ne da manya-manyan tashoshi da na sama da na ruwa kuma har mun kai musu na’ura da za su yi amfani da ita na wuccin-gadi wanda daga nesa ma kana iya auna zafin jikin mutum ba tare da ka je kusa da shi ko taba shi ba, kuma za mu kara karfafa su, yanzu haka hatta inda babu alamun wannan cutar mun kai jami’an mu kuma har ma sukan tsaya su yi tambaya ko da mai zazzabi? sai a ware shi.
Aminiya: Baya ga mu’amulla da mai wannan cutar, ta wace hanya kuma ake kamuwa da wannan cutar?
Gwarzo: To da farko dai wannan cutar ta dabbobi ce asalinta, tana ciki jemagu masu cin ‘ya’yan itace, kuma tana cikin su birai, irin su gwaggwon biri da barewa da gada, ta cin wadannan namun daji ana iya kamuwa, kuma ba cin wadannan dabbobin ba ne matsala, a’a taba ruwan jikin su ma illa ne, wato a dauko naman wadannan dabbobin a rike shi da hannu ko bayan gidansu ko amansu, duk suna dauke da wannan cutar. Amma yanzu zancen da ake yi shi ne, cutar ta riga ta tsallaka shinge ta wuce cikin dabbobi ta fado kan jama’a kuma ta fara yaduwa a tsakanin dan adam da dan adam, shi ne ya sa za ka ga idan mutum ya kamu zai shafa wa wadansu, kuma a irin haka ne wani dan kasar Liberiya ya zo ya shafa wa likitanmu, shi ya sa yanzu haka muna nan muna kula da ragowar ma’aikata, domin an kai jininsu a auna kuma da zaran an dawo da sakamakon Minista zai yi bayani game da haka.
Aminiya: To beraye da kyenkyasai fa, ana samun wannan cutar daga gare su, ganin su ma suna kusa da jama’a sosai?
Gwarzo: A’a, bera da kyenkyeso ba su yadawa, domin duk karance-karance na ban ga inda aka ce suna yada wannan cutar ba, daga bayyanan annobar har yanzu babu inda aka ce suna yada wannan cutar, sai dai su din ma cuta ne, don haka a yi kokari a guje musu.
Aminiya: Ganin cewa likitoci na yajin aiki kuma gashi har yanzu ana nan ana binciken, to yaya za ku yi da wannan kalubalen?
Gwarzo: Ai ba kowa ne yake yajin aikin ba, akwai ragowar ma’aikatan asibiti, kuma akwai kilitoci masu zaman kansu, kana akwai likitocin da suka dawo suna bada gudunmowa irin ta sa kai, hatta kwamitin da muke aiki da su a Legas akwai likitoci da ma’aikatan asibiti da suka kawo kansu suka ce sun zo ne domin su bada gudunmowar su ga wannan aikin. Kuma a Abuja yanzu nake harhada yadda za mu samar da wuraren fadarkawa, kuma na yi magana da wadansu kwamishinoni da gwamnonin domin daukar matakan ko- ta-kwana game da yaki da wannan cutar, ban tsammanin cewa wannan yajin aikin zai yi tasiri ga aikin da muke yi yanzu.
Aminiya: Yanzu wane hali jihar Legas take ciki game da wannan binciken da kuke yi?
Gwarzo: Bincike kam ana nan ana yi, domin ko ba na kwana guda ba ne za a yi a ce an tsaya, ana kan yi, kuma duk wanda aka bincika ko da an ga bai da shi za a jira har bayan kwana 21 kana za iya cewa lallai bai da wannan cutar.
Aminiya: An ce wadansu ‘yan kasar Liberiya sun shigo Najeriya domin su ga Fasto T.B.Joshua domin wai ya warkar da su, shin ko kuna sane da wannan ?
Gwarzo: An tura wakilan gwamnati sun je sun yi magana da shi T. B. Joshua, saboda ana tsoron kar masu wannan cutar su shigo ya hada da su bai sani ba, ina tabbatar maka cewa duk motar da za ta shigo daga kasar waje sai an auna mutanen, domin muna da na’ura mai tantance masu zazzabi wanda ake iya ganin cewa suna dauke da wannan cutar, sai dai idan ta barauniyar hanya ce suka shigo, shi kuma Fasto mun fada masa ya kula.
Aminiya: Ganin yadda wannan cutar ta yo caa kan jama’a ko akwai wadataccen maganin ta ko kuma rigakafi?
Gwarzo: Ai ba ma Najeriya ba, duk duniya ma har yanzu ba a gano maganinta ba, ba a kuma samo rigakafinta ba, sai dai magunguna da za a ba mutum domin cutar ta lafa jikinsa ya yi kwari kuma kaifinta ya ragu ainun. Muna sa ran cikin mutane 10 da ke kamuwa da cutar daga 1-5 suna rayuwa.
Aminiya: Ke nan ba a warke wannan cutar kwata-kwata?
Gwarzo: Ana dai samun sauki sosai, kuma mutum zai samu kwarin jikinsa.
Aminiya: An ce wai namijin goro na maganin wannan cutar, shin da gaske ne?
Gwarzo: Ni ma na ji wannan jita-jitar, a matsayina na ma’aikacin kimiyya da kiwon lafiya ba zan iya cewa da kai wannan jita-jitar gaskiya ne ba, illa iyaka jita-jita ce, amma mutum kar ya yi amfani da jita-jita, ya yi amfani da abin da yake sahihi, kar mutum ya bata lokacinsa wajen cin namijin goro ya je ya bata cikinsa da cin abin da ba zai yi masa amfani ba, domin wannan ba harka ce ta shaci fadi ba.
Aminiya; Wace shawara za ka bai wa mutane game guje wa kamuwa da wannan cutar?
Gwarzo: Shawarar da zan bai wa mutane ita ce kada su yarda wannan firgicin ya ratsa su su ki daukar matakin da ya dace, mutane su mike tsaye su yi duk abin da ya dace wajen ganin sun yi abin da ya kamata su yi game da guje wa kamuwa da wannan cutar, musammam ta neman sani game da wannan cutar. Kuma yanzu abin da muka hango shi ne, wadansu yanzu haka sun wasa wukar su domin su cuci talakawa game da wannan cutar ta hanyar cewa suna da maganin cutar, duk wanda ya ce ya samu maganin ta to ya kawo dakin bincike domin a tantance sahihancin maganin kafin ya fara sayar wa jama’a