Cutar huhun dabbobi ta kashe shanu 368 a Jihar Kaduna

Dabbobi 754 na cikin mawuyacin hali   Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da barkewar cutar huhun dabbobi wadda ta yi sanadiyyar mutuwar shanu 368 a sassan jihar, baya ga wasu 764 da ke fama da ciwon da ya watsu a sassan jihar. Jami’in watsa labarai na Ma’aikatar Noma da Gandun Daji, Malam Dahiru Abdullahi, ya […]

Cutar huhun dabbobi ta kashe shanu 368 a Jihar Kaduna
  • Dabbobi 754 na cikin mawuyacin hali

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da barkewar cutar huhun dabbobi wadda ta yi sanadiyyar mutuwar shanu 368 a sassan jihar, baya ga wasu 764 da ke fama da ciwon da ya watsu a sassan jihar.

Jami’in watsa labarai na Ma’aikatar Noma da Gandun Daji, Malam Dahiru Abdullahi, ya ce cutar kan kama huhun dabbobi ne da suka hada da shanu da jakauna da makamantansu, ya ce ma’aikatarsu kan kula da dabbobin tare da ba su magungunan da suka dace.

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da magunguna da allurai inda ta raba ga asibitocin dabbobi da ke kananan hukumomin jihar,” inji shi, sannan ya kara da cewa sashin kula da dabbobi na ma’aikatar ya gudanar da binciken jinin dabbobin da suka kamu da ciwon a dakunan gwaje-gwaje inda ya ce sakamakon gwajin ya tabbatar musu da yaduwar cutar inda ma’aikatar ta tashi haikan wajen daukar matakan dakile cutar daga ci gaba da yaduwa.

Binciken da aka gudanar na nuna cewa, an gwada ciwon ya barke ne a wasu sassa na kananan hukumomin Kachiya da Kagarko da Kubau da ke jihar.

Ya ce, tuni gwamnatin jihar ta samar da kwararrun likitocin dabbobi da suke ci gaba da lura da dabbobin da suka kamu da ciwon tare da dakile ci gaba da yaduwar cutar a tsakanin dabbobin.