Cutar kansa ta kashe mutumin farko da ya warke daga cutar Kanjamau

Mista Timothy Ray Brown, mutumin farko da a tarihi ya warke daga cutar Sida mai karya gaskuwar jiki wadda aka fi sani da Kanjamau, ya rasu sakamakon cutar kansa. Mista Timothy wanda aka fi sani da Berlin Patiens ya warke ne a shekarar 2007 bayan ya yi fama da cutar tun daga shekarar 1995. ‘Air […]

Cutar kansa ta kashe mutumin farko da ya warke daga cutar Kanjamau

Mista Timothy Ray Brown, mutumin farko da a tarihi ya warke daga cutar Sida mai karya gaskuwar jiki wadda aka fi sani da Kanjamau, ya rasu sakamakon cutar kansa.

Mista Timothy wanda aka fi sani da Berlin Patiens ya warke ne a shekarar 2007 bayan ya yi fama da cutar tun daga shekarar 1995.

Bayan warkewarsa, Kungiyar Cutar Kanjamau ta Duniya ta ce hakan ya nuna akwai alamar za a samar da maganin cutar ta HIV.

Mista Timothy, wanda dan asalin Amurka ne mai shekara 54 ya kamu da cutar ce lokacin yana garin Berlin na kasar Jamus sannan daga bisani ya kamu da kansar jini.

Ya warke ne bayan an yi amfani da fasahar canja bargo.

An yi masa aikin canja bargo na farko ne a shekarar 2007, inda tun a lokacin cutar HIV din ta fara tafiya, amma ta kansa ta ki ragewa.

An kara masa aikin bargon bayan ya samu wani a shekarar 2008, wannan ma bai yi aiki ba.

A bara ce kansar ta dawo da karfi, sannan ya rasu a jiya Laraba.