Cutar kansar bakin mahaifa na kashe mata 8,000 a Najeriya 

OPV wata sabuwar cutar daji ce ta da ke kama bakin mahaifa, kuma takan kashe mata akalla 8,000 a Najeriya a duk shekara

Cutar kansar bakin mahaifa na kashe mata 8,000 a Najeriya 

Wata mara lafiya a gadon asibiti. (Tsohuwa ajiya).

Akalla mata 8,000 ne suke mutuwa a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar dajin bakin mahaifa a duk shekara.

Babban Sakataren hukumar lafiya matakin farko a Jihar Gombe, Abdurrahman Shu’aibu ne ya sanar da hakan ga ’yan jarida jim kadan bayan kammala wani taron fadakarwa.

Abdurrahman Shu’aibu ya ce, OPV wata sabuwar cutar daji ce ta da ke kama bakin mahaifa, kuma takan kashe mata akalla 8,000 daga cikin wadanda suka kamu da ita a duk shekara a Najeriya.

Sai dai ya bayyana cewa akwai allurar riga-kafin wacce ake yi wa mata kanana masu shekaru 9 zuwa 14.

Babban sakataren ya ci ga da cewa a baya ana yin allurar riga-kafin ne a asibitoci masu zaman kansu a kan kudi Kimanin Naira dubu 60.

Amma yanzu an samar da allurar riga-kafin kyauta a asibitocin gwamnati kuma tuni aka kaddamar, sanna ba ta da wata illa.

A cewarsa, a watan Oktoban da ya gabata aka shigo da allurar a wasu jihohin Najeriya 16.

Amma Jihar Gombe da wasu jihohi 22 sai a ranar 27 ga watan nan na Mayu ne za a shigo da nasu allurar riga-kafin.

Shu’aibu ya kara da cewa dalilin shirya taron shi ne domin fadakar da jama’a da kuma gabatar musu da allurar saboda cigaban da aka samu.

Ya ce akwai kwamiti da aka kafa da za su yi yawon fadakar da mutane muhimmancin allurar riga-kafin cutar dajin bakin mahaifa a gidajen Radiyo da sauran kafofi.

Daga nan ya ce idan aka gwada mace aka ga tana dauke da cutar za a yi mata magani, idan ta kama a yi mata aiki ne ma za a yi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos