Cutar koda ta mamaye jihohin Barno da Yobe da Kano da Jigawa
Karuwar kamuwa da cutar koda a yankin Arewa maso gabas da suka hada da jihohin Barno da Yobe da Adamawa da kuma Jigawa da Kano ya janyo asarar rayuka. Abin da yake haddasa cutar mafutsarar wacce take shafar galibi matasa an alakantata da shan magungunan kashe radadi da na hawan jini barkatai. Wani mazaunin Maiduguri, […]
Karuwar kamuwa da cutar koda a yankin Arewa maso gabas da suka hada da jihohin Barno da Yobe da Adamawa da kuma Jigawa da Kano ya janyo asarar rayuka.
Abin da yake haddasa cutar mafutsarar wacce take shafar galibi matasa an alakantata da shan magungunan kashe radadi da na hawan jini barkatai.
Wani mazaunin Maiduguri, Jibrin Martins wanda ya yi magana da Aminiya ya ce ya yi asarar abokanensa takwas sakamakon kasa yin fitsari a kwanana nan.
“Halin da muke ciki abin fargaba ne don cikin watanni 15 abokanaina takwas sun mutu. Sun rasu ne sakamakon kamuwa da cutar koda. Dukkansu suna tsakanin shekaru 30. Hatta iyalansu sun kadu sosai”. Inji Jibirin
Ya bayyana cewa lamarin ya haifar da rudani sosai a yankunan.
Kwararre kuma shugaban fannin cututtukan da suka danganci mafutsara a asibitin Malam Aminu Kano wanda har ila yau shi ne babban likita a asibitin Rasheed Shekoni da ke garin Dutse, Farfesa Aliyu Abdu ya yi magana kan yaduwar cutar a yankin Hadeja.