Cutar kurkunu na addabar mutane a Jihar Nasarawa
Mazauna kauyen Wakama da ke Yankin Akun a karamar Hukumar Nasarawa-Eggon a Jihar Nasarawa sun yi kira ga gwamnatin jihar ta kai musu dauki don kawo karshen cutar kurkunu a rafinsu. Wasu mazauna kauyen da wakilinmu ya zanta da su sun ce sun dade suna fuskantar annobar cutar ba tare da gwamnati ta kawo musu […]
Mazauna kauyen Wakama da ke Yankin Akun a karamar Hukumar Nasarawa-Eggon a Jihar Nasarawa sun yi kira ga gwamnatin jihar ta kai musu dauki don kawo karshen cutar kurkunu a rafinsu.
Wasu mazauna kauyen da wakilinmu ya zanta da su sun ce sun dade suna fuskantar annobar cutar ba tare da gwamnati ta kawo musu karshensa ba.
Mukaddashin Mai Unguwar kauyen Mista Emmanuel Ayingbu ya ce jama’ar kauyen sun fi shekara 10 suna fuskantar cutar kurkunu. Kuma a cewarsa suna matukar bukatar taimakon gwamnati, “Wannan rafi shi ne kawai muke da shi a nan inda muke debo ruwan sha da na ayyukan yau da kullum. Amma mun kasa amfani da shi kasancewar kurkunu ya mamaye shi. Wadannan kwari da ke haifar da kurkunu hadari ne ga rayuwanmu a halin yanzu don suna jawo mana matsala a kullum. Kuma sukan fito daga rafin zuwa gidajenmu su jawo mana illa,”inji shi.
Ya bukaci gwamnatin jihar da karamar hukumarsu su gina musu rijiyoyin burtsatse a yankin don magance cutar kurkunu a yankin baki daya. Ya yi kuma bukaci gwamnatin jihar ta kai musu dauki cikin gaggawa domin a cewarsa a halin yanzu al’ummar yankin da dama suna fama da cutar kurkunu sosai.
daya daga cikin wadanda cutar ta shafa mai suna Malle Elijah ya ce shiga wani kwari ne ya jawo kurkunu ya kama shi a kafa, inda nan take zazzabi ya kada shi. Ya ce ya yi bakin kokarinsa don magance lamarin, amma bai yi nasara ba, inda sai da aka kai shi Asibitin Janar da ke Akwanga kafin ya samu sauki.
Ya ce duk da yake a wasu lokuta gwamnati kan turo ma’aikatan kiwon lafiya da magunguna ana ba su, sai dai a cewarsa magungunan suna kwantar da lamarin ne na wani lokaci ba sa warkar da shi.
Wakilinmu ya ziyarci sakatariyar yankin Akun don jin ta bakin daraktan kiwon lafiya kan lamarin, amma bai samu shi a ofishinsa ba kuma lambar wayarsa ba ta tafiya a lokacin.