Cutar Kurona: An dage Gasar Nahiyar Turai zuwa 2021
Hukumar Kwallon Kafar Turai ta sanar da dage Gasar Kofin Nahiyar Turai wato Euro na bana zuwa badi. Gasar wadda da za a fara daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga Yuli, yanzu za a fafata shi ne daga 11 ga Yuni zuwa 11 ga Yulin badi. A cewar hukumar, “lafiyar masu ruwa da […]
Hukumar Kwallon Kafar Turai ta sanar da dage Gasar Kofin Nahiyar Turai wato Euro na bana zuwa badi.
Gasar wadda da za a fara daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga Yuli, yanzu za a fafata shi ne daga 11 ga Yuni zuwa 11 ga Yulin badi.
A cewar hukumar, “lafiyar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni yana da matukar muhimmanci. Sannan kuma dagewar za ta taimaka wajen ganin gasanni da aka dage saboda cutar an samu kammala su.
“Don haka duk wasannin UEFA har da na sada zumunta na kungiyoyi da kasashe, na mata da maza duk an dakatar da su har sai mama-ta-gani.
“Mun kafa kwamiti da zai duba yanayin tsarin kowace gasar da kuma fito da tsarin da ya kamata a bi a kan kakar bana.”