Cutar Kurona: An dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dage bikin wasanni na kasar na shekarar 2020 a matsayin matakin hana yaduwar cutar Kurona, wanda aka shirya yi a jihar Edo. Ministan wasanni Sunday Dare, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a shafinsa na kafar sadarwa na twitter. Sunday, ya ce an dauki wannan matakin ne bayan da […]

Cutar Kurona: An dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020

Ministan Wasanni Sunday Dare, a ofishinsa da ke filin wasa na kasa MKO Abiola Abuja

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dage bikin wasanni na kasar na shekarar 2020 a matsayin matakin hana yaduwar cutar Kurona, wanda aka shirya yi a jihar Edo.

Ministan wasanni Sunday Dare, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a shafinsa na kafar sadarwa na twitter.

Sunday, ya ce an dauki wannan matakin ne bayan da ministan lafiya da na wasanni sun gana da Shugan Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Talata da safe.

Kafin dage wasannin an shirya fara bikin wasannin ne daga ranakun Lahadi 22 ga Maris 2020 zuwa Laraba 1 ga Afrilu 2020.