Cutar Kurona: An daura aure cikin minti biyu a China
Wadansu ma’aurata ’yan kasar China sun shiga kundin tarihi, sakamakon gudanar da bikin daurin aure cikin minti biyu kacal, kuma mutum shida kadai suka halarci bikin sanye da abin rufe hanci, don kauce wa daukar cutar numfashi na Kurona (Coronavirus ko Cid-19). Ango Zhang Long da amaryarsa Chen Diao da suka fito daga Lardin Shandong […]
Wadansu ma’aurata ’yan kasar China sun shiga kundin tarihi, sakamakon gudanar da bikin daurin aure cikin minti biyu kacal, kuma mutum shida kadai suka halarci bikin sanye da abin rufe hanci, don kauce wa daukar cutar numfashi na Kurona (Coronavirus ko Cid-19).
Ango Zhang Long da amaryarsa Chen Diao da suka fito daga Lardin Shandong da ke Gabashin China, sun yi gaggawar halartar bikin da ya gudana a harabar kotu, tare da mahaifin amaryar a matsayin babban bako da mahaifiyarta a matsayin wadda ta dauki hotunan bikin.
Ma’auratan sun bi umarnin gwamnati ce ta tsayawa a gida don kauce wa shiga cinkoson jama’a, sakamakon bullar cutar Kurona. Mutanen kasar China da dama sun dage bukukuwansu sakamakon bayyanar cutar, amma Zhang da Chen suka amince cewa ranar bikin ba za ta kubce musu ba.
“Muna cikin wani mawuyacin lokaci ne na rigakafin kamuwa da cutar, don haka muka yanke shawarar kin gayyatar baki zuwa zauren da za a yi shagalin bikin,” inji ango Zhang. “Bayan wadannan shirye-shiryen abu mafi muhimmanci shi ne kowa ya kasance cikin murna,” inji shi.
A ranar bikin, angon Zhang, ya rufe hancinsa inda ya raka amaryarsa har zuwa gida da ke birnin Licha, daya daga cikin biranen Kingdao.
Amaryar ta sha ado, amma sai dai ta rufe fuskarta a matsayin kariya daga cutar da ta’addabi kasar. A cewar angon, “Ban san wane irin jan baki ma amaryar ta sanya ba.”
Mahaifin amaryar ne ya jagorancin daurin auren, wanda bai wuce minti biyu ba. Zhang ya ce, surukina ya yi bayani cikin sauri, ya kuma gode wa iyayen da suka halarci bikin. Sannan ya ce, an kammala daurin auren. Mu ma’auratan ba a ba mu damar yi wa baki jawabin godiya ba,” inji Zhang.
Kafin bullar cutar Kurona Zhang, ya shirya za a aiwatar da bikin kamar ake yi a al’adar kasar. Ya tanadi kujerun liyafar abinci na mutum 50 da motoci 20 don harkokin bikin, sannan ya gayyato abokansa na musamman.
Amaryar ta ce, “An soke duk wasu shirye-shirye da aka yi don shagalin bikin, angona ya kashe kudi kalilan ne kawai don aura ta, ban da mu da rashin yin shagalin bikin ba, saboda na amince da shi a matsayin masoyina kuma zabina.”
A hanyar kai amarya zuwa gidan mijin sun wuce shingayen binciken jami’an tsaro inda aka yi musu gwajin lafiyar jikinsu, sannan bayan gwajin an tabbatar da kalau suke.
Chen ta ce. “Duk da ’yan uwa da dama ba su halarci, bikin ba. Amma ina da yakinin wadansu sun yi mana addu’a a zuciyar su.”
Mazauna birnin da dama sun mika sakon murnar auren ta hanyar shafin muhawara na WeChat.