Cutar Kurona: An tsare kyanwar da aka kai Indiya daga China

Wata kyanwa da aka dauko ta daga kasar China bisa kuskure a cikin kwantainan kaya na fuskantar barazanar maida ta gida don tsoron yaduwar cutar Kurona. An tsare kyanwar ce a tashar jiragen ruwa na Chennai da ke kasar Indiya, kwana 20 da suka wuce bisa zargin cewa tana iya yada cutar Kurona a kasar, […]

Cutar Kurona: An tsare kyanwar da aka kai Indiya daga China

Kyanwar da aka tsare

Wata kyanwa da aka dauko ta daga kasar China bisa kuskure a cikin kwantainan kaya na fuskantar barazanar maida ta gida don tsoron yaduwar cutar Kurona.

An tsare kyanwar ce a tashar jiragen ruwa na Chennai da ke kasar Indiya, kwana 20 da suka wuce bisa zargin cewa tana iya yada cutar Kurona a kasar, inda ake cin naman kyanwa da sauransu.

A martanin da suka mayar, masu fafutikar ganin an kyautata kula da dabbobi a kasar (PETA) ta bakin manaja mai kula da harkokin dabbobi a Indiya, Rashmi Gokhale, ya aika sako zuwa ga mahukuntan tashar jiragen ruwa na Chennai, inda ya shaida musu cewa gwaje-gwaje sun nuna kyanwar ba ta iya kamuwa ko yada cutar ta Kurona.

A nata bangaren, Kungiyar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Amurka a shafinta na Intanet ta ce, “Manya-manyan hukumomin kula da lafiya na duniya sun yi nuni da cewa, dabbobin gida ba sa fuskantar barazanar kamuwa da cutar Kurona (COBID-19).”

Sai dai sashin da aka killace kyanwar tuni suka bada shawarar maida kyanwar inda ta fito.

PETA ta ce, zai yi matukar wuya a gano inda kyanwar ta fito har ta shige akwatin daukar kayan. Kuma ta kara da cewa, abu ne mai wuya kyanwar ta jure tafiyar kwana 10 zuwa 20 da aka yi da akwatin daga kasar China zuwa Indiya ba tare abinci ko ruwa ba.

Jiragen ruwa da suke tafiya zuwa Chennai daga Indiya sukan yi zango a kasashen Singapore da Kolombo da wasu wurare a kan bude akwatuna saboda sauke kayayyaki. Hakan na nufin cewa, kyanwar ka iya shigewa a daya daga cikin wuraren da jiragen suke zango.

Hukumar PETA ta kara da cewa, ana kashe kyanwa saboda amfani da namanta ko gashi, kuma hakan ka iya faruwa da kyanwar idan aka maida ta kasar China.

PETA, ta mika bukatar a ba ta damar hada hannu da hukumomi saboda samar wa kyanwar wani mazauni a kasar Indiya, idan hukumomin lafiya sun kammala bincikensu.