Cutar Kurona ta sake yaduwa zuwa Aljeriya, Brazil da Faransa

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana ta bayyana fargabarta ga  Najeriya sakamakon bullar cutar a Nahiyar Afirka, kamar yadda aka samu rahoton cutar ranar Laraba a kasar Brazil. A Faransa an samu rahoton mutuwar wani sanadiyyar kamuwa da cutar. Ma’aikatar lafiya ta kasar Aljeriya, ta sanar da rahoton bullar cutar Kurona. Yayin da a karon […]

Cutar Kurona ta sake yaduwa zuwa Aljeriya, Brazil da Faransa

Wasu da cutar Kurona ta bulla a kasar su

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana ta bayyana fargabarta ga  Najeriya sakamakon bullar cutar a Nahiyar Afirka, kamar yadda aka samu rahoton cutar ranar Laraba a kasar Brazil.

A Faransa an samu rahoton mutuwar wani sanadiyyar kamuwa da cutar.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Aljeriya, ta sanar da rahoton bullar cutar Kurona. Yayin da a karon farko aka samu bullar cutar da ake kira COVID-19 a Nahiyar Afirka a kasar Masar.

Jim kadan, an samu bullar cutar karon farko a Kudancin Amurka a kasar Brazil, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar.

A ranar Laraba an tabbatar da bullar cutar ta kama mutum 81,109 a duk duniya, yayin da aka samu rahoton karin yaduwar cutar da ya kai adadin 871 daga ranar Talata zuwa Laraba duk a wannan makon.