Cutar Kurona: Za a rufe makarantu a jihohin Arewa 9

Gwamnonin Arewa Maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun bayyana aniyarsu na rufe makarantu da ke yankin na kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Kurona a yankin. Gwamnonin sun ce za a rufe makarantun ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris. Wannan mataki da gwamnonin suka dauka ya biyo bayan kasidar bayan taron da […]

Cutar Kurona: Za a rufe makarantu a jihohin Arewa 9

Taron Gwamnonin Arewa

Gwamnonin Arewa Maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun bayyana aniyarsu na rufe makarantu da ke yankin na kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Kurona a yankin.

Gwamnonin sun ce za a rufe makarantun ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

Wannan mataki da gwamnonin suka dauka ya biyo bayan kasidar bayan taron da suka yi ne a jihar Kaduna wanda shugaban Kungiyar Gwamnoni ta Arewa maso Yamma, Aminu Masari da shugaban Gwamnonin Arewa ta  tsakiya ‎Sani Bello, suka rattaba hannu kuma aka rabawa manema labarai a jihar.

Jihohin tara sun hada da: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Neja, Sakkwato, da Zamfara.

Sun ce, gwamnonin za su dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumar gudanar da jarabawa ta kasa.