Cutar kwalara ta hallaka mutum 7 a sansanonin ’yan gudun hijira na Maiduguri
Akalla mutum 7 ne hukumomi suka tabbatar da rasuwarsu, yayin da sama da mutum 200 ke kwance a asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a sansanonin ’yan gudun hijira na garejin Muna da Unguwar Dala Lawanti da ke garin Maiduguri, cikin mako biyun da suka gabata. Duk da akwai ma’aikatan kiwon lafiya a akasarin sansanonin da […]

Akalla mutum 7 ne hukumomi suka tabbatar da rasuwarsu, yayin da sama da mutum 200 ke kwance a asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a sansanonin ’yan gudun hijira na garejin Muna da Unguwar Dala Lawanti da ke garin Maiduguri, cikin mako biyun da suka gabata.
Duk da akwai ma’aikatan kiwon lafiya a akasarin sansanonin da suke kula da lafiyar ’yan gudun hijirar musamman mata da kananan yara cutar ta amai da gudawa ta halaka tare da galabaitar mutane a sansanonin.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Dokta Abubakar Hassan, ya ce ambaliyar ruwan saman da aka samu a sansanin Muna ya dada habakar cutar, kuma akwai cinkoson mutane a sansanin da koramu suka kewaye. “To amma tun lokacin da abin ya faru jami’anmu na kiwon lafiya suke ta kokarin shawo kan lamarin, tare da hadin gwiwar jami’an kiwon lafiya na kungiyon agaji na duniya. Kuma alhamdulillahi yanzu an samu nasarar shawo kan lamarin, sai dai cutar ta hallaka mutum 7, yayin da kimanin mutum 200, suke kwance a asibitoci daban-daban suna karbar magunguna. Kuma mun mike tsaye wajen tsabtace wadannan sansanoni kamar tsotse ruwan da ya yi ambaliya, muna rokon jama’a su taimake wajen yaki da wannan cuta ta hanyar tsabtace muhallansu da kula da yadda kananan yara suke gudanar da rayuwarsu,’ inji shi.