Cutar Kwalara ta kashe mutane 45 a Kano

Shugaban hukumar, Farfesa Muhammad Adam Abbas, ya ce masu cutar kwalara 45 sun rasu ne a 28 daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

Cutar Kwalara ta kashe mutane 45 a Kano

Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano

Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 45 a sakamakon kamuwa da cutar Kwalara.

Shugaban hukumar, Farfesa Muhammad Adam Abbas, ya ce masu cutar kwalara 45 sun rasu ne a 28 daga cikin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

Ya shaida wa wani taro da ma’aikatar lafiya ta jihar ta shirya cewa cutar kwalara tana saurin yaɗuwa a wuraren da ke da ƙazanta ko rashin kula da lafiyar abinci.

Ya shawarci jama’a da su riƙa tsaftace hannayensu tare da kula da tsaftar muhalli dan na abinci ta hanyar wanke ’ya’yan itatuwa da kayan lambu da sauransu kafin su ci.

A cewarsa, gwamnatin jihar tana ɗaukar matakan dakile yaɗuwar cutar ta hanyar kashe ƙwayoyin cuta a cikin ruwa a yankunan da aka samu ɓullar cutar.