Cutar kyandar biri ta bulla a kasar Kanada

Ana bincike kan karin mutum 17 da ake zargi sun kamu da cutar a yankin Montreal

Cutar kyandar biri ta bulla a kasar Kanada

Hukumomin lafiya sun tabbatar da kamuwar mutum biyu da cutar kyantar biri a kasar Kanada.

Mutanen biyu da aka gano dauke da cutar a ranar Alhamis da dare ya kara adadin masu dauke da ita a nahiyar Turai da Arewacin Amurka, lamadin da ya haifar da zullumi kan cutar mai yaduwa da kuma kisa.

“A cikin daren nan (Alhamis) aka sanar da Lardin Quebec cewa samfur din jini da aka karba daga NML na dauke da cutar Kyandar Biri.

“Wadannan su ne mutum biyu na farko da aka samu suna dauke da kwayar cutar a kasar Kanda,” kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar.

Hukumomin kasar sun cewa ana gudanar da bincike kan wadansu mutum 17 da ake zargin suna dauke da kyautar a yankin Montreal, wanda shi ne birni mafi girma a Lardin Quebec.

Akalla mutum 20 ne aka tabbatar sun kamu da cutar mai yaduwa da kuma kisa a yankin Turai da Arewacin Amurka, daga farkon watan Mayu.

Hakan dai ya haifar da damuwa da fargabar cewa cutar da ta samo asali daga yankin Yammacin Afirka tana yaduwa a duniya.

Kyandar biri bakuwar cuta ce, wadda alamominta suka hada da zazzabi, ciwon jiki, kuraje masu kama da na cutar kyada a fuska da hannu, sai kuma kumburi.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta ce, “ana iya yada cutar kyandar biri ta hanyar saduwa da ruwan jiki, ruwan ciwon, tufafi ko shimfida da ruwan ciwon ya taba.”

Amma ta bayyana cewa sanadirai masu kashe kwayoyin cuta na gida na iya kashe kwayar cutar.